Home Mulki Tinubu Ya Sake Nada Mele Kyari A Matsayin Shugaban NNPCL

Tinubu Ya Sake Nada Mele Kyari A Matsayin Shugaban NNPCL

114
0
Tinubu and Mele Kyari

Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya sake nada Mele Kolo Kyari a matsayin shugaban kamfanin mai na NNPCL.

A watan Yunin 2019, tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fara nada Kyari a matsayin shugaban kamfanin na NNPCL.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litnin, Kakakin Tinubu, Ajuri Ngelale, ya ce nadin zai fara aiki daga ranar Juma’a 1 ga watan Disambar 2023.

Shi ne ya gaji marigayi Maikanti Baru, wanda ya yi ritaya daga aiki kafin rasuwarsa.

Cikin sanarwar, Ngelale har ila yau ya ce Tinubu ya kafa kwamitin gudanarwar kamfanin wanda Cif Pius Akinyelure zai jagoranta a matsayin shugaban da ba na gudanarwa ba.

Sauran Shugabannin sun hada da:

(3) Alhaji Umar Isa Ajiya — Shugaban Kudi

(4) Mr. Ledum Mitee — Shugaba bana gudanarwa ba

(5) Mr. Musa Tumsa — Shugaba bana gudanarwa ba

(6) Mr. Ghali Muhammad — Shugaba bana gudanarwa ba

(7) Prof. Mustapha Aliyu — Shugaba bana gudanarwa ba

(8) Mr. David Ogbodo — Shugaba bana gudanarwa ba

(9) Ms. Eunice Thomas — Shugaba bana gudanarwa ba

Bayan haka shugaba Tinubu ya nada Manyan Sakatarori kamar haka:

(10) Mr. Okokon Ekanem Udo — Babban Sakatare Ma’aikatar Kudi

(11) Amb. Gabriel Aduda — Babban Sakatare Ma’aikatar Mai

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here