Home Tsaro Tinubu ya naɗa sabbin hafsoshin tsaro a Najeriya

Tinubu ya naɗa sabbin hafsoshin tsaro a Najeriya

220
0

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗa sabbin manyan hafsoshin tsaron Najeriya da kwamandojin fadar shugaban ƙasa.

Matakin na zuwa ne bayan sabon shugaban ya sanar da matakin sallamar hafsoshin da ke jagorantar rundunonin tsaron ƙasar daga aiki nan take.

Wata sanarwa da Mista Willie Bassey, daraktan yaɗa labarai a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya fitar, ta bayyana Mallam Nuhu Ribaɗu a matsayin Mashawarcin shugaban ƙasa kan harkar tsaro wato National Security Adviser.

An yi ta muhawara kwanan baya, lokacin da Tinubu ya sanar da sunan tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC a matsayin mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkar tsaro.

Da wannan sanarwa, Mallam Nuhu Ribaɗu dai zai gaji Manjo Janar Babagana Mongunu (mai ritaya).

Shugaban Najeriyar dai ya naɗa Manjo Janar C.G Musa a matsayin babban hafsan tsaro, bayan sallamar Laftanal Janar Lucky Irabor.

Sai kuma Manjo Janar T. A Lagbaja a matsayin babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya, inda ya canji Laftanal Janar Faruk Yahaya.

Haka zalika, Rear Admiral E. A Ogalla ya zama babban hafsan sojin ruwa na Najeriya, inda ya maye gurbin Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo.

Akwai kuma Air Vice Marshal H.B Abubakar a matsayin sabon babban hafsan rundunar sojojin sama na ƙasar, inda ya gaji Air Marshal Oladayo Amao.

Ƙarin manyan jami’an tsaron har da DIG Kayode Egbetokun a matsayin Babban Sufeton ‘Yan sandan Najeriya, inda ya maye gurbin Usman Alƙali Baba.

Haka kuma sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya naɗa Manjo Janar EPA Undiandeye a muƙamin babban hafsan tattara bayanan sirri na tsaro wato Defence Iintelligence.

Sauran naɗe-naɗen da Shugaba Tinubu ya amince da su, akwai Kanal Adebisi Onasanya a matsayin kwamandan bataliyar tsaron fadar shugaban ƙasa.

Sai Laftanal Kanal Moshood Abiodun Yusuf, matsayin sabon kwamandan bataliyar tsaron fadar shugaban ƙasa runduna ta 7 da ke Asokoro a birnin Abuja.

Haka zalika, an naɗa Laftanal Kanal Auwalu Baba Inuwa, kwamandan bataliyar tsaron fadar shugaban ƙasa, runduna ta 177 da ke jihar Nasarawa.

Tinubu ya kuma naɗa Laftanal Kanal Mohammed J. Abdulkarim matsayin kwamandan bataliyar tsaron fadar shugaban ƙasa, runduna ta 102, da ke Suleja a jihar Neja.

Yayin da Laftanal Kanal Olumide A. Akingbesote zai karɓi ragamar aiki a matsayin kwamandan bataliyar tsaron fadar shugaban ƙasa, runduna ta 176 da ke Gwagwalada a Abuja.

Ƙarin manyan jami’an sojojin tsaron fadar shugaban ƙasa da Bola Tinubu ya amince da naɗin su, har da Manjo Isa Farouk Audu a muƙamin kwamandan kula da dakarun atilare na fadar shugaban ƙasa.

Sai Kaftin Kazeem Koyejo Hamzat a matsayin kwamandan dakarun soji masu tattara bayanan sirri a fadar shugaban ƙasa.

Akwai kuma Manjo TS Adeola a matsayin kwamandan kula da makamai a fadar, yayin da Laftana A. Aminu zai kasance matsayin mai taimaka masa.

Sanarwar ta ce hafsoshin da sauran jami’an da aka naɗa kan muƙaman, za su ci gaba da kasancewa a matsayinsu har zuwa lokacin da za a tabbatar da su kamar yadda tsarin mulkin Tarayyar Najeriya ya tanada.

Ƙarin naɗe-naɗen su ne:

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kuma naɗa Hadiza Bala Usman a mataimakiya ta musamman a kan ayyukan daidaita manufofi.

Hannatu Musan Musawa kuwa, ya naɗa ta matsayin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin al’adu da bunƙasa harkokin nishaɗantarwa.

Haka kuma, Shugaba Tinubu ya naɗa Sanata Abdullahi Abubakar Gumel a muƙamin babban mataimaki na musamman kan harkar Majalisar Dattijai.

Yayin da Hon. Olarewaju Kunle Ibrahim ya kasance babban mataimaki na musamman kan harkar Majalisar Wakilai.

Sai kuma, Adeniyi Bashir Adewale, mutumin da Shugaba Tinubu ya naɗa kan muƙamin Babban Kwamturola na riƙa a hukumar hana fasa-ƙwauri ta Najeriya (Customs). (BBC).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here