Home Uncategorized Tinubu ya koma gidan zaɓaɓɓen shugaban ƙasa

Tinubu ya koma gidan zaɓaɓɓen shugaban ƙasa

204
0

Zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya koma gidan da kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanadar wa zaɓaɓɓen shugaban ƙasa gabanin rantsar da shi a matsayin sabon shugaban Najeriya a ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa.

A wani saƙon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Bayo Onanuga mataimaki na musamman ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya ce Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima sun koma gidan da aka tanadar wa shugaban ƙasa mai jiran-gado da aka fi sani da ‘Defence House’.

A ranar 24 ga watan Afrilu ne Tinubu ya koma Najeriya bayan hutun kwanaki sama da talatin da ya yi a birnin Paris. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here