Home Siyasa Tinubu ya buƙaci shugabannin Afrika su mutunta ƴancin dimokuraɗiyya

Tinubu ya buƙaci shugabannin Afrika su mutunta ƴancin dimokuraɗiyya

177
0
Tinubu p

Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga ɗaukacin shugabannin Afrika da su mutunta ƴancin dimokuraɗiyya da doka-da-oda da kuma wanzuwar siyasa.

Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a taron tsakiyar shekara na gamayyar Kungiyoyin Haɗin Kan Afirka da na rassan ƙungiyoyin tattalin arzikin ƙasashen yankin Afirka da ke gudana a Nairobi, babban birnin ƙasar Kenya.

Tinubu ya buƙaci mahukuntan ƙasashen na Afrika da su tabbatar sun mutunta batun sake sabunta mulkin dimokuraɗiyya.

Shugaban Najeriyar wanda kasance sabon shugaban kungiyar Ecowas, ya ce ya kamata a yi watsi da batun juyin mulki a faɗin nahiyar, musamman ma wannan lokaci da ake fama da rashin tsaro da sauyin yanayi da kuma annobar korona.

Ya ce abin takaici ne ganin cewa duk da kasancewar Yammacin Afrika sahun gaba wajen ɗaɓɓaka dimokuraɗiyya da kuma kyakkyawar shugabanci, ita ke gaba a yankin wajen amfani da hanyoyi da suka saɓa wa kundin tsarin mulki don sauya gwamnati.

Ya kuma yi gargaɗin cewa yawaitar kifar da gwamnatoci da ake samu a Afrika, na barazanar kawo rashin zaman lafiya da tsaro, da janyo talauci da ɗaiɗaita mutane wajen raba su da muhallansu.

”Tsakanin 2020 zuwa yanzu, Afria ta fuskanci juyin mulki guda shiga da kuma guda uku wanda ba a samu nasara ba. Hakan na janyo tarnaki ga tsarin dimokuraɗiyyar mu a Afrika.

“Don haka, na ke kira ga ɗaukacin shugabannin Afrika da su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun mutunta ƴancin dimokuraɗiyya da kuma doka-da-oda don tabbatar da ɗorewar siyasa a nahiyar,” in ji Tinubu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here