Home Taron Harsashen Yanayi Na Kasashen Sahel: An Shawarci Manoma Da Mutanen Da Ke Yankin Da Su Rinka Amfani Da Rahoton Don Gujewa Asara

Taron Harsashen Yanayi Na Kasashen Sahel: An Shawarci Manoma Da Mutanen Da Ke Yankin Da Su Rinka Amfani Da Rahoton Don Gujewa Asara

Mahalarta Taron na yakin Arewacin Africa da ake yiwa lakabi da kasashen Sahel sun shawarci manoma da saura mazauna yankin da su bawa rahoton kasashen na kowacce shekara muhimmanci domin gujewa asara ta rai da dabbobi da kayan amfanin gona.

Sun bayar da wannan shawara ne Jiya Litinin a Abuja a wurin taron wannan shekara ta 2024 da ajeriya ke daukar nauyi.
Suka ce makasudin taron shine don su karawa juna sani tare da sanar da manoman yankin harsashe na yanayi da su ka gano domin bawa manoma shawarwari na irin abubuwan da za su Noma don gujewa asara.
Mai kula da hasashen yanayi ta Najeriya wato (Nimet), ta ce Akwai yiwuwar Damina ta faɗi a ƙarshen watan Mayu me kamawa ko kuma ta shiga farkon watan yuni.
Babban Jami’i Hukumar kula da hasashen yanayi ta Najeriya (Nimet) James Adamu ne ya bayyana hakan a yayin taron masu ruwa da tsakin bangaren Muhalli na ƙasashen yankin Sahel.
  1. IMG 20240422 WA0071
Kuma dai Ƙasashen yankin Sahel ɗin suna gudanar da taron ne domin neman mafita, akan hasashen da ake yi na ɗaukewar ruwan sama da wuri a daminar dake tafe.
James ya ƙara da cewa, saukar Daminar ita ce zata kawo ƙarshen zafin da ake fama dashi a halin yanzu, harma ya buƙaci Al’umma da su ci-gaba da shuka bishiyu domin magance ƙaruwar matsalar ɗumamar yanayin da ake fuskanta a kowacce shekara.
Haka kuma Hukumar ta buƙaci Manoma da su yi shuka da wuri kuma su sami iri me inganci, domin yin kanda-garki akan hasashen ɗaukewar daminar da wuri da akayi.
A nasa ɓangaren Jami’in daya wakilci Jamhuriyar Nijar SaidiTounni, ya ce babu shakka sauyin yanayin ya haddasa matsaloli a harkar nomar Nijar dama Mutuwar Dabbobi.
  1. IMG 20240422 WA0072
Haka kuma Tounni ya ce akwai alamun taron nasu ya haifarwa ƙasashen nasu kyakykyawan sakamako, ta fuskar rage yawan matsalar da ake hasashen sauyin yanayin zai haifar.
Ita ma wakiliyar ƙasar Ghana a wurin taron Francisca Martey, ta ce amfanin haɗuwar tasu wuri guda shine domin musayar dabaru da fasashohi, ta yadda za’a magance matsalolin da sauyin yanayin yake haifarwa ƙasashen su.
Martey ta kuma jaddada muhimmanci samun irin da yake yi da wuri, domin gudun samun matsalar amfanin gona.
Mahalarta taron dai zasu fitar da sakamako na ƙarshen taron, a ranar Jumu’a da zasu kammala taron domin samar da mafitar ƙalubalen ɗaukewar daminar musamman ta fannin samar da Abinci.