Home Siyasa Tantance Yanyatsu: Mata Karku Wahalar Da Na’urar BVAS – INEC

Tantance Yanyatsu: Mata Karku Wahalar Da Na’urar BVAS – INEC

196
0

Tun bayan komawa tafarkin dimokradiyya ake fuskantar matsaloli dabam-daban a lokacin zabe a Najeriya, matsalolin da suka hada da ba yara da shekarunsu basu kai ba damar zabe, aringizon kuri’u sakamakon rashin alkaluman da ke nuna takamaimai yawan mutanen da aka tantance a rumfunan zabe, da sauransu.

Tarin matsalolin da ake fuskanta a lokacin zabe suka sa hukumar zabe ta Najeriya ta INEC yin kwaskwarima ga tsarin gudanar da zaben saboda ya zama cikin sauki.

Ci gaba da ake samu ta fannin kimiyya na taka rawa wajen sauye-sauyen, yanzu ta kai ga ana amfani ne da na’urar BVAS da ke tantance masu kada kuri’a.

Jami’a a sashen yada labarai a hukumar INEC a birnin tarayya Abuja Zainab Baba Aminu, ta yi karin bayani game da na’urar BVAS. Tana mai cewa wata fasahar zamani ce da INEC ta kirkiro domin tantace mai kada kuri’a da tabbatar da cewa katin shi ne.

A Najeriya dai mata su ke da kaso mai yawa na masu kada kuri’a a lokacin zabe, kuma su ne aka sani da yin kwalliyar lalle da kuma ayyukan da suka hada da daka, surfe da sauransu, da hakan ka iya kawo cikas wajen tantance zanen yatsunsu da na’urar BVAS. Zainab Baba Aminu ta ja hankalin mutane musamman mata game da hakan.

Wasu mata da Muryar Amurka ta zanta da su domin jin irin matakan da suka dauka don guje wa fuskantar duk wani kalubale na tantancewa a lokacin kada kuri’a, sun ce za su tabbata ba su saka lalle ba kuma su dauki duk matakan da suka dace don kare kuri’arsu.

Ana dai sa ran fara gudanar da babban zabe a Najeriya a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here