Home Siyasa Tantance Ministoci: Yadda Majalisar Dattawa Ta Marawa A.T.M Gwarzo Baya

Tantance Ministoci: Yadda Majalisar Dattawa Ta Marawa A.T.M Gwarzo Baya

256
0
ATM Gwarzo

Bayan da Tshohon Mataimakin Gwamman Kano, Abdullhai  Tijjani Muhammad (A.T.M) Gwarzo kuma wanda Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya zaba don ya kasance da ga cikin Ministocinsa ya tsaya a gaban zauren Majalisar Dattawa ranar Juma’a (04/08/2023) mutane da yawa ba su yi mamakin irin yabon da ya samu ba da ga Sanatoci musamman da ga Jihar Kano.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya bawa A.T.M Gwarzo dama na ya gabatar da kansa a gaban  Sanatoci 109; ganin yawan Yan Majalisar bai razana shi ba, a matsayinsa na gogaggen dan siyasa kuma nutsatstse kamu mai ilimi.

Ba tare da bata lokaci ba, A.T.M Gwarzo ya bayar da takaitaccen tarihin sa da kuma irin gogewarsa a siyasa da aikin gwamnati.

Nan take, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ya daga hannu, a inda Shugaban Majalisar ya ba shi dama na ya yi Magana. A inda ya ce, “Mai girma Shugaba, wannan mutum da yake tsaye gabanka kuma a gaban dukkan Yan Majalisa sananne ne a guna da dukkan mutanen Jihar Kano, sabo da haka ba ya bukutar dogon bayani”

Sanata Barau ya kara da cewa, Abdullahi Gwarzo ya taba rayuwar al’umarsa ta fannoni da dama lokacin da ya ke Shugaban Karamar Hukuma a Gwarzo; ya yi aikace – aikace na kawo cigaba ga jama’arsa. “Ni sheda ne akan haka”. Inji Barau

Ya ce bayan Gwarzo ya yi Shugaban Karamar Hukumar, ya yi Shugaban Kungiyar Kananan Hukumomi ta Najeriya wato ALGON, Kano  kuma ya yi Kwamishina; sannan bayan haka ya zama Mataimakin Gwamna karkashin, Sanata Malam Ibrahim Shekarau.

Sanata Barau, ya ce wadannan aiyuka da ya yi, Mai Girma Shugaba manuniya ce ta irin gogewarsa a siyasa da sanin aikin gwamnati da Shugabanci; kuma ba‘a taba samun sa da wani gazawa ba wajen gudanar da aiyukan sa.

Sabo da haka, na ke neman Majalisa da Yan Majalisa da su kyale shi da ya risinawa Majalisa ya wuce. Ina fatan Yan uwana Yan Majalisa zasu goyi bayan wannan bukata tawa” inji Barau.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce ya gamsu da maganganun, Mataimakin Shugaban Majalisa, Sanata Barau Jibrin amma zai bawa Yan uwansa Yan Majalisa da ga Kano dama su ma suyi Magana.

Take, Sanata Akpabio ya bawa Sanata Kawu Sumaila dama na ya yi magana, inda ya nuna goyan bayansa ga dukkan maganganu da Sanata Barau ya yi; inda shima ya ce ya goyi bayan a kyale A.T.M Gwarzo da ya risinawa Majalisa ya wuce.

Shima Sanata Rufa’I Hanga, bai bata lokaci ba wajen nuna goyon bayan zabin Shugaban Kasa na A.T.M Gwarzo; inda ya ce zabi ne wanda ya dace; sabo da haka ya goyi bayan a kyale Gwarzo ya risinawa Majalisa ya wuce.

Sai dai Shugaban Majalisar Dattawa, ya ce kafin ya nemi amincewar Majalisa akan bukatun su, zai bawa Abdullahi Gwarzo dama na da ya amsa tambayar Sanata Ekon Samson wanda ya nemi cewa Mai zai yi na daban idan ya zama Minista wajen gyara kananan Hukumomi ganin yadda ya ke da kwarewa a mulkin kananan hukumoni?

A.T.M Gwarzo cikin nutsuwa ya ce” amsar tambayar sa abu biyu ne kawai, na farko, bawa Kananan Hukumomi Yancin Cin gashin Kai; na biyu kuma Yancin Hukumar Zabe a Jihohi, idan anyi haka za’a samu cigaba da zaman lafia”.

Nan ta ke, Shugaban Majalisar Dattawa ya ce, mu ma wannan shi ne ra’ayin Majalisa. A inda ya tambayi Yan Majalisar ko sun amince da bukatun Sanatocin Jihar Kano na abar zababben Ministan ya risina ya wuce? Ta ke su ka amince baki daya.

Abun da ya yi saura shine idan Majalisar ta kammala tantancewar za ta sake zama ranar Litinin don ta amince da sunayen Ministocin 48 da Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya tura mata da ta tantance ta kuma amince masa da ya nada su a gurare daban daban.

Koda ya ke Majalisar ta ce ba lallai dukkan sunayen da ta tantance za ta amince da su ba; amma akan batum A.T.M Gwarzo, Bahaushe na cewa Juma’ar da za tai kyau, tun da ga Laraba ake ganewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here