Home Siyasa Takarar Shugabancin Majalisar Wakilai: Gamaiyar Yan’takara Bakwai Sun Karyata Ficewar Daya Da...

Takarar Shugabancin Majalisar Wakilai: Gamaiyar Yan’takara Bakwai Sun Karyata Ficewar Daya Da Ga Cikin Su

138
0

Gamaiyar Yan’takarar Shuagabancin Majalisar Wakilai sun karyata fecewar Alasan Ado Doguwa da ga cikin su; “ har yanzu muna tare a matsayin tsintsiya guda,” inji Hon. Aminu Jaji.

Hon. Aminu Jaji ya sanar da haka ne a wajen taron kaddamar da takarar sa da aka gudanar a dakin taro na Lagos dake Otel din Transcorp dake Abuja a jiya Alhamis.

Hon.  Jaji yace, kansu a hade yake kuma sunyi amanna cewa daya da ga cikin su ne suke sa ran zai zama shugaban Majalisar Wakilai ta Goma domin kuwa sun yi amanna da aki dojin su iri daya ne kuma a shirye suke su marawa duk wanda Allah ya bawa shugabanci a cikin su baya.

Yace, ba za su yarda a kakaba masu Shugaba na jeka na yika ba kuma sun yarda cewa Zababben Shugaban Kasa Ahmad Bola Tinubu ba shi da hannu a wannan tsarin da aka yi.

“mun yi amanna cewa, Bola Tinubu dan Siyasa ne ya san cewa siyasa tana bukatar tuntuba da neman amincewar yan takara kamar yadda ya ke a cikin tsarin Mulkin Jam’iyar APC sabo da haka ba bu hannun sa a cikin wannan tsari da akayi”

Sauran Yan’takarar sunyi jawabi a inda suka nuna goyan bayansu da junan su da yin alkawarin tafiya tare na ganin sun cimma nasara a wannan fafutuka da suke yi na neman Shugabancin Majalisar  Wakilai ta Goma.

Taron na su ya samu halartar da yawa da ga cikin zababbun Yan Majalisar Wakilai tsofaffi da Sababbi wadan da suka nuna goyon bayan su da wannan tafiya suke yi.

A jawabin sa Mataimakin Shugaban Majlisar Wakilai Hon. Wase ya nuna cewa wannan tafiya ta sub a gudu ba ja da baya kuma sune suke da rinjaye na zababbun Yan Majalisa wanda hakan zai ba su daman a lashe wannan zabe da za’a yi.

Yace, ba za su yarda masu shan jinni su shugabance su ba, wadan da kansu kawai suka sani basu damu da mutumci Yan uwansu ba. Sabo da haka za suyi duk mai yiwuwa wajen ganin sune suka sami nasara a zaben da za’a yi.

Daga karshe yayi kira ga Jam’iyar APC da Shugaban Kasa Zababbe, Bola Ahmad Tinubu das u sakarwa da Demokiradiyya mara ta barin su su zabi wanda suke so ya shugabance su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here