Home Labaru masu ratsa Zuciya Sojojin Najeriya sun ceto mutum 386 da suka shafe shekaru 10 cur...

Sojojin Najeriya sun ceto mutum 386 da suka shafe shekaru 10 cur hannun Boko Haram a Dajin Sambisa

86
0
Sambisa 360

Aƙalla mutum 386 yawancin su mata da ƙananan ne Sojojin Najeriya suka ceto, bayan sun shafe shekaru 10 a hannun ‘yan Boko Haram, cikin Dajin Sambisa.

Kwamandan Riƙo na Sojojin Runduna ta 7, AGL Haruna ne ya bayyana haka, lokacin da yake jawabi ga manema labarai, a gefen Dajin Sambisa, cikin Ƙaramar Hukumar Konduga, bayan da ya tarbi zaratan sojojin da suka shafe kwanaki 10 suna kakkaɓar ‘yan ta’adda cikin Sambisa.

Burgediya Janar Haruna ya ce sojojin sun yi ‘sharar daji’ ne suka kakkaɓe ɓurɓushin ‘yan ta’addar da ke cikin dajin, wasun su kuma suka yi gaggawar yin saranda.

“Ƙoƙarin mu dama shi ne a kakkaɓe ɓurɓushin ‘yan ta’addar da suka rage a cikin dajin Sambisa, sannan kuma mu baiwa masu aniyar yin saranda damar miƙa wuya.

“Da yawan su sun yi saranda, kuma muna sa ran wasu da dama za su ci gaba da yin saranda.

“Sannan kuma mun ceto fararen hula. Zuwa jiya dai mun ceto farar hula 386, kuma ina da tabbacin cewa adadin waɗanda aka ceto ɗin zai ƙaru zuwa yau.” Cewar Haruna.

Ya jinjina wa zaratan sojojin dangane da irin juriya da kishi da ƙwarewar su wajen gudanar da aikin su. (PREMIUM TIMES).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here