Home Uncategorized Sojojin Isra’ila sun fara kutsawa wasu unguwannin Gaza

Sojojin Isra’ila sun fara kutsawa wasu unguwannin Gaza

215
0
Israila shiga unguwanni

Sojojin Isra’ila sun ce sun fara kai samame wasu unguwannin Zirin Gaza yayin da dakarunsu ke shirin kai gagarumin farmaki ta ƙasa.

Mai magana da yawun sojin Isra’ilar ya ce manufar yin hakan shi ne domin kawar da ‘ƴan ta’adda’ da kuma kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su.

Sanarwar na zuwa daidai lokacin da Falasɗinawa ke barin arewacin Gaza a ƙoƙarinsu na cika umarnin da Isra’ila ta basu na barin yankin.

Daruruwan mashina da manyan motoci ɗauke da katifu da sauran kayan amfanin yau-da-kullum ke ficewa daga Arewacin Gazar, yayin da wasu da dama suke tafiya a ƙasa. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here