Home Tsaro Sojoji Sun Fatattaki ’Yan Bindiga, Sun Kwato Rokoki A Zamfara

Sojoji Sun Fatattaki ’Yan Bindiga, Sun Kwato Rokoki A Zamfara

238
0

Dakarun rundunar hadin gwiwa ta ‘Operation Hadarin Daji’, sun yi nasarar fatattakar ’yan bindiga da dama bayan wani samame da suka kai a kauyukan Kagara, Gidan Fadama, Gangara, Tseika, Malamawa da Zango Kamarawa a Kananan Hukumomin Talata Mafara da Shinkafi a Jihar Zamfara.

Aminiya ta gano cewa, a ranakun Talata da Laraba, sojoji sun fara aikin shara a kan sansanonin ’yan bindiga da a yankunan, inda suka yi artabu da ’yan ta’addan, tare da kashe da dama daga cikinsu, suka lalata sansanoninsu.

Sojojin sun kuma kwato rokoki, bindigar PKT guda, alburusai, bindiga kirar AK-47 guda uku tare da lalata babura 19 na ’yan ta’addan.

Sun kuma kai wani samame a yankin Dogon Awo-Lamba Bakura da ke Karamar Hukumar Bakura, inda suka dakile harin da ’yan bindiga suka kai a babbar hanyar zuwa Sakkwato.

A baya dai ’yan fashin dajin sun tare babbar hanyar Sakkwato zuwa Gusau da nufin sace matafiya, amma sai sojojin suka yi gaggawar zuwa wurin tare da korar su. (Aminiya).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here