Home Siyasa Siyasar Kano: Yadda APC da NNPP su ka koma ga Allah kafin...

Siyasar Kano: Yadda APC da NNPP su ka koma ga Allah kafin hukuncin kotu

236
0
Addua NNPP

Hausawa kan ce komai ya yi zafi, maganinsa Allah!

Ga dukkan alamu, manyan jam’iyyun Kano biyu, sun mayar da al’amarin nasu ga Allah, daidai lokacin da suke jira kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar ta sanar da hukuncin da ta yanke a nan gaba.

Hukuncin kotun dai yana da matuƙar muhimmanci ga jam’iyyun NNPP mai mulki a ƙarƙashin jagorancin Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da APC mai adawa wadda Dr. Abdullahi Umar Ganduje ke jagoranta.

Kwankwaso da Ganduje dai, manyan aminan juna ne da suka yi siyasar ubangida da yaronsa a jihar, kafin su rikiɗe su koma manyan abokan adawar juna.

Magoyan bayan jam’iyyar APC mai adawa a Kano, suna ci gaba da tarukan addu’o’i da saukar Alƙur’ani a mazaɓu da ƙananan hukumomi, bayan da yawansu sun yi azumin nafila a ranar Litinin.

Matakin na zuwa ne bayan tun da farko, ‘ya’yan jam’iyyar NNPP mai mulkin Kano sun gudanar da irin wannan taron addu’o’i, bayan gudanar da sallah a ranakun ƙarshen makon da ya gabata.

Ɗaruruwan magoya bayan NNPP ne suka taru a filin wasa na Ƙofar Na’isa sanye da jajayen huluna ranar Asabar don gudanar da salloli da kuma addu’o’un neman nasara.

Su ma gomman magoyan APC sun gudanar da saukar Ƙur’ani a Masallacin Sheikh Ahmadu Tijjani da ke Ƙofar Mata da kuma addu’o’i a ranar Lahadi.

Haka nan, magoya bayan Nasiru Gawuna na APC sun yi wani taron a mazaɓarsa ta Gawuna da ke cikin ƙaramar hukumar Nassarawa, inda suka yanka dabbobi.

Yunƙurin nasu na zuwa ne yayin da ake jiran hukuncin da kotun za ta yanke a ƙarar da APC da ɗan takararta Nasiru Yusuf Gawuna suka shigar don ƙalubalantar nasarar gwamna mai-ci Abba Kabir Yusuf da NNPP.

Siyasar Kano ta ƙara zafi ne bayan alƙaliyar kotun, Mai Shari’a Flora Ngozi Azinge, ta yi zargin cewa ana yunƙurin ba su cin hanci da zimmar sauya hukunci. Sai dai ba ta faɗi jam’iyya ko mutanen da take zargi ba.

Hukumar zaɓen Najeriya, Inec, ta ayyana Abba Kabir a matsayin wanda ya lashe zaɓen na watan Maris bayan ya samu ƙuri’a 1,019,602, sai kuma Nasiru Gawuna na APC – mai mulkin jihar a lokacin – da ya zo na biyu da ƙuri’a 890,705.

Wannan ne karo na uku da jam’iyyar adawa ke doke mai mulki a jihar Kano cikin shekara 24 – bayan komawa mulkin dimokraɗiyya a 1999 – don kuwa, an yi hakan a 2003, da 2011.

Addua APC

‘Wanda ma yake zalunci ya yi addu’a ballantana wanda aka zalunta[?]’

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ce ke riƙe da madafun iko lokacin da NNPP ta doke ta a zaɓen na watan Maris, wanda hakan ya sa take zargin ‘yan adawar da yin maguɗi da kuam “zalinci”.

APC ta ce ta lura da yadda ‘yan NNPP suka rungumi addu’o’i “duk da cewa su ne azzaluman”, shi ya sa ita ma ta umarci ‘ya’yanta su koma ga Allah.

“Sai muka ga wanda ma yake zalinci ya hyi addu’a ballantana wanda aka zalinta, shi ya sa muka yanke hukuncin fawwala wa Allah, mu kai kuka gare shi don ya share mana hawaye,” kamar yadda Sakataren APC na Kano Abdullahi Sarina ya shaida wa BBC.

Sai dai ya ce rungumar addu’o’in ba ya nufin “gazawa”, yana mai cewa “shari’a mace ce da ciki, ba a san abin da za ta haifa ba.

“Duk wanda ya shiga shari’a kuma yake cewa yana da tabbas zai yi ci [nasara], to bai san mece ce shari’a ba. Duk abin da aka ce gaibu ne, to sai a bar wa Allah hukuncinsa.”

Jagororin jam’iyyar sun umarci magoya bayansu a faɗin Kano baki ɗaya su ci gaba da yin azumin.

‘Sun yarda kuɗi ne zai yi musu komai’

Lokacin da Inec ta bayyana NNPP a matsayin wadda ta yi nasara, shi ne karo na farko da jam’iyyar ta ci zaɓen gwamna a Najeriya baki ɗaya. Hasali ma ita kaɗai ce kujerar gwamnan da take da ita a faɗin ƙasar.

Ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, shi ne jagoran jam’iyyar a ƙasa da kuma Kano bayan ya yi gwamnan jihar tsawon shekara takwas.

“A matsayin na waɗanda muka nema a wajen Allah kuma ya ba mu, dole ne mu yi amfani da duk damar da muke da ita don tseratar da shi,” a cewar Shugaban NNPP na Kano Hashim Sulaiman Dungurawa.

Ya ƙara da cewa al’ummar Kano suke dubawa kuma dalilin da ya sa suka saka addu’o’i ke nan a gaba saboda zargin APC za ta yi amfani da kuɗi wajen sauya hukuncin.

“Waɗannan mutanen akwai abin tsoro a tare da su,” in ji shi. yana mai cewa “mutane ne da suka yarda kuɗi zai iya yi musu komai, ba su tsoron kallon mutunci da darajarsu wajen yin abin da ya kamata”.

Jumirin jira, zanga-zanga, da umarnin ‘yan sanda

A yanzu dai a iya cewa dukkan manyan jam’iyyun siyasar na Kano na zaman jiran makomarsu ne sakamakon matakin kotun sauraron ƙararrakin zaɓe na jingine bayyana hukuncinta.

A ranar Litinin 21 ga watan Agusta duka ɓangarorin biyu suka gabatar da jawabansu na ƙarshe a gaban kotun, amma Mai Shari’a Azinge ba ta saka ranar da za a sanar da hukuncin ba.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, kotun ba ta faɗi ranar da za tas ake zama ba.

Lamarin ya sa rundunar ‘yan sandan Kano ta fitar da sanarwar haramta “duk wani nau’i na zanga-zanga” a faɗin jihar saboda bayanan sirrin da ta ce ta samu na ƙoƙarin NNPP da APC wajen yin amfani da “magoya baya na haya”.

“Ya kamata al’umma su sani cewa muna da labarin APC da NNPP na yunƙurin ɗaukar magoya baya na haya da sunan ‘yan ƙungiyar fararen hula kuma ba tare da samun izini daga ‘yan sanda ba,” in ji rundunar.

Sai dai duk da hanin dubban magoya bayan jam’iyyun sun gudanar da zanga-zanga a titunan jihar. Mabiya ɗariƙar Kwankwasiyya na NNPP ne suka fi yawa a kan titunan birnin suna masu zargin APC da amfani da ƙarfi a kan alƙalan kotun. APC ta musanta zargin.

“Muna da yaƙinin cewa alƙalai a Kano za su yi adalci a shari’o’in da ke gabansu,” kamar yadda aka ji Gwamnan Kano Abba Kabir na faɗa wa masu zanga-zangar a ranar Litinin ɗin.

Zargin bai wa alƙalai toshiyar baki

A ‘yan kwanakin da suka gabata rahotanni sun ambato Mai shari’a Flora Azinge na cewa karo na biyu ke nan wani alƙalin kotun na kai mata ƙorafi a kan yadda wasu lauyoyi da ke cikin ƙararrakin da kotun ke sauraro, suna ƙoƙarin ba su cin hanci.

Zargin na babbar alƙaliyar na nuna tsananin rufewar idon ‘yan siyasar, ta yadda wasu ke ƙoƙarin sayen nasarar da suka kasa samu ta halastacciyar hanya daga jama’ar da za su mulka.

Ba a saba jin alƙalai na fitowa bainar jama’a suna kokawa kan ƙoƙarin ba su toshiyar baki ko cin hanci a Najeriya ba.

Sai dai kamar yadda aka saba, a wannan karo ma duk manyan masu ruwa da tsaki sun sun tsame kansu daga zargin da mai shari’ar ta yi.

Gwamnatin Kano ce ta fara fitowa tana nesanta kanta, sai dai ba ta tsaya a nan ba, ta riƙa yin ishara da sashen takwararta mai adawa wato APC.

Da alama zarge-zargen ba da cin hanci sun damu ƙungiyar lauyoyi ta Kano, wadda shugabanta na jihar, Barista Sagir Sulaiman Gezaw,a ya rubuta wa kotun wasiƙa yana neman ta bayyana sunayen lauyoyin da suka yi yunƙurin bai wa alƙalan toshiyar baki. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here