Home Siyasa Shugabancin Majalisar Wakilai: Yadda Yan Takara 6 Suka Bijirewa Umarnin Jam’iyar...

Shugabancin Majalisar Wakilai: Yadda Yan Takara 6 Suka Bijirewa Umarnin Jam’iyar APC

158
0

Duk da yake Jam’iyar APC ta fidda wadanda take so su yi takara a matakin Shugaba da Mataimaki na Majalisar Dattijai da ta Wakilai, masu sha’awar shugabancin majalisar na cigaba da nuna rashin amincewar su da wannan tsari.

A jiya Juma’a Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilar, Hon. Ahmed Idris Wase ya kaddamar da takarar sa na sha’awar shugabancin Majalisar  ta Wakilai, a dakin taro na Otel din Transcorp da ke Abuja.

Gangamin taron na neman takarar tasa ya sami tagomashi na halartar Yan takar biyar wadanda suka nu na rashin amincewar su da matakin da uwar Jam’iyar APC ta dauka na tsayar masu da Tajuddeen Abas daga Arewa ta Tsakiya da kuma Benjamin Kalu daga Kudu ma so Gabas.

Hon. Idris Wase yace, “ shugabancin Majalisar Wakilai wannan karon lokaci na ne” cikin harshen Yarbanci kamar Yadda Zababen Shugaban Kasa, Ahmed Bola Tinubu ya rinka fada lokacin da ya ke takara.

Wase, ya yi bayani irin sadaukarwar da ya yi na janyewa wasu aMajalisa ta takwas da ta tara, wanda hakanne ya kawo Kakakin Majalisar ta tara, Hon. Femi Gbajabiamila a matsayi shugaba. Sabo da haka yace yanzu lokaci yayi da za a ramawa Kura aniyar ta inji shi.

Ya cigaba da cewa, matakan da Kwamitin  Zartarwa na Jam’iyar APC ya dauka na fidda yan takar ya sabawa kuddin mulkin Jam’iyar ta APC domin akwa bukatar a sami sahalewar dukkan Yan takara kafin a tsaida Yan takara amma ba’yi hakan ba.

Hon. Wase yace, yan takara na Shugabancin Majalisar Wakilai su shida da suka hada kai manuniya cewa su ke da rinjaye kuma da yardar Allah yaci zabe ya gama na Shugabacin Majalisar Wakilai a wannan Majalisar ta goma.

Dukkan Yan takarar guda shida sun amince su hada kai a matsayin  tsintsiya guda wajen ganin sun sami nasara a wannan gwagwarmaya da su ke yi na samun shugabancin Majalisa ta goma da ga cikin yan takarar akwai Hon. Muktar Aliyu Betara, da Hon. Princess Miriam Onuaha da Hon. Aminu Sani Jaji.

A hirar da mu ka yi da Hon. Aliyu Betara yace, halartar su wannan gangami na Hon. Wase manuniya ce ta cewa sun ci zabe sun gama. Yace kawunan su a hade ya ke kuma a shirye suke su marawa wani daga cikinsu ba ya ya dare shugabancin Majalisar ta goma.

Taron ya sami halartar yan majalisa da dama da zababbu da wadan da ba zababbu ba kuma dukkannun su sun yaba da halaye na gari na Hon. Ahmed Idris Wase tun ma kafin ya zama Mataimakin Shugaban Kakakin Majalisar ta tara.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here