Home Siyasa Shugabancin Majalisa Ta 10: Daram Damdam Inji Sanata Hanga

Shugabancin Majalisa Ta 10: Daram Damdam Inji Sanata Hanga

151
0
Sen. Hanga

Sanata Rufa’i Hanga, Dan Majalisar Dattawa Mai Wakiltar Kano ta Tsakiya ya baiyana cewa, Shugabancin Akpabio da Tajuddeen Abas ya zama shugabanci na dindindin duk da cewa Shugaban Jam’iyar APC na Kasa, Abdullahi Adamu ya kalubalanci hakan.

Sanata Hanga ya baiyana haka ne ranar Alhamis a hirarsa da Yanjaridu a ofishin sa da ke Majalisar a Abuja.

Ya ce, tsarin dokokin Majalisar Taraiya ne ya bawa Yan Majalisar dama da su zabi shugabanni  wadanda za su jagoranci Majalisar. Ya ce lokaci ya wuce da za a kakabawa Majalisar Shugabanci na jeka na yi ka.

Hanga ya kara da cewa, Yan Majalisar suna wakiltar al’umar su ne ba wai Jam’iya ba duk da cewa a karkashin tutar Jam’iyar suka zama zababbu amma hakkin Jam’iya akansu shine su kare manufofi na Jam’iya ba wai shugabanci ba.

Sanatan ya ce ana zaben shugabanni ne da kaso daya bisa uku amma kuma tsige shugabanci ana bukatar kaso biyu bisa uku na dukkannin Yan Majalisar sabo da haka zaiyi wuya a cire ko a ruguje shugabancin da suka rigaya suka zaba.

Sanata Hanga ya ce duk da cewa ya na daga Jam’iyar NNPP wacce ta kasance da ga cikin marasa rinjaye sun gamsu da yadda aka zabi shugabancin Majalisar kuma za su bawa shugabancin dukkan goyon baya muddin akwai adalci a cikin sa.

Ya ce zasu marawa Shugabancin Akpabio goyon baya wajen ganin  Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta sami nasara wajen gabatar da aiyuka da za su kawo chigaba ga Yan Najeriya.

Shima Sanata Aliyu Wadada dag a Jihar Nasarawa ya goyi bayan yadda aka zabi shugabancin Majalisar kuma ya ce a shirye ya ke a matsayinsa na Shugaban Jam’iyar SDP a Majalisar da ya goyawa Akpabio baya wajen ganin an gudanar da aiyuka da za su kawo cigaba a kasarnan.

Sanata Wadada ya goyi bayan Kudurin da Sanata Kawu Sumaila ya kawo wanda ya bukaci da a gaggauta dakatar da Jinginar da Tashar Jirgin Sama ta Malam Aminu Kano sabo da an saka son zuciya wajen amincewa da kwangilar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here