Home Diplomasiyya Shugabancin Ecowas: Abubuwa uku da Tinubu zai mayar da hankali a kansu

Shugabancin Ecowas: Abubuwa uku da Tinubu zai mayar da hankali a kansu

272
0
ECOWAS Tinubu

Kamar dai yadda aka saba, bayan zaɓen duk wani shugaba a kowanne mataki, shugaban zai tashi ya yi godiya ya kuma bayyana alƙawuran da zai cika a yayin jagorancinsa.

Irin haka ce ta faru ga shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu bayan zaɓar da aka yi masa a matsayin sabon shugaban ƙungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, Ecowas.

Kakakin Shugaban Najeriya Abdul’aziz Abdul’aziz ya yi wa BBC ƙarin bayani game da zaɓen Tinubu da kuma bayanan da ya gabatar bayan zaɓen nasa.

“Ƙimar Najeriya na ƙara bunƙasa a idanun ƙasashen Afrika da Duniya baki ɗaya, kuma wannan dalili ya sa suka bai wa Shugana Bola Ahmed Tinubu jagorancin wannan ƙungiya.

“Ka tuna bai yi wata biyu ba cikakku kan mulki amma darajar ƙasar da kuma shi kansa ta sa suka ba shi jagorancin,” in ji Abdul’aziz.

Tinubu ya zayyana abubuwa uku da zai bai wa muhimmanci waɗanda suka haɗa da:

Tsaro da zaman lafiya

Duk da cewa abu ne sananne cewa yankin ƙasashen da suka haɗa ƙungiyar na fama da matsalar tsaro amma Tinubu ya jadada buƙatar kawo ƙarshen matsalar saboda muhimmancin da take da shi.

“Game da zaman lafiya da tsaro, barazanar takai matakin ƙololuwa da ya zama wajibi a ɗauki matakan gaggawa domin shawo kan ƙalubalen,” in ji sabon shugaban.

“Babu shakka ƙarancin zaman lafiya a yankunanmu zai ci gaba da daƙile ci gabanmu, kuma yankin mu ya ci gaba da zama a baya.

A wannan gaɓa, dole mu nuna damuwa da ci gaba da amfani da tsare-tsaren da muka kawo domin ganin ƙarshen matsalar tsaro,”

Matsalolin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai irinsu, Boko Haram da ISWAP ko shakka babu na haifar da koma baya a ci gaban yankin, in ji Tinubu.

A cewarsa matsalar na ƙara faɗaɗa zuwa ƙasashe da yankunan da a baya ba su fuskantarta.

Tabbatar da dimokraɗiyya

Wannan maudu’i na ɗaya daga cikin batutuwan da suka mamaye taron da ECOWAS ta gudanar karo na 63 a Guinea Bissau.

Saboda wasu daga cikin mambobin ƙungiyar ba sa ƙan turbar dimokradiyya, ba da gangan ba, sai domin sun faɗa hannun sojojin juyin mulki.

Ƙasashen Mali da Burkina Faso da kuma Guinea waɗanda mambobin ƙungiyar ne dukkansu sojoji ke jagorantarsu a yanzu.

Da wannan dama da ya samu Bola Tinubu na son amfani da hanyoyin shiga tsakani domin samun damar mayar da su turbar dimokraɗiyya.

Za a yi wannan ne ta hanyar tabbatar da gudanar da zaɓuka, ta yadda fararen fula za su zaɓi shugabannin da za su jagorance su kan tafarkin siyasa.

Abdul’aziz ya ce “so yake ya tabbatar da an daina samun juyin mulki tsakanin sojoji, tsarin dimokraɗiyya na daga waɗanda ake so a tabbatar, a bai wa mutane damar kawar da mutanen da ba su yi musu ba a matsayin jagorori.”

Kuɗin bai ɗaya

Abdul’aziz ya ƙara da cewa Tinubu ya yi tsokaci kan kuɗaɗen bai ɗaya da aka jima ana maganarsu, waɗanda ko shakka babu samar da su zai haɓɓaka kasuwanci tsakanin ƙasahen yankin.

Samar da ƙuɗin zai taimaka wajen sauƙaƙa wahalhalun kasuwanci da ke tsakanin ƙasashen da duka mambobin wannan ƙungiya ne.

Kazalika zai sauƙaƙa wahalhalun da ake fuskanta wajen musayar kuɗin ƙasashen waje marasa tabbas da kuma faɗuwar darajar kuɗaɗen cikin gidan ƙasahen ECOWAS.

A 2020 ne wasu daga cikin ƙasashen ECOWAS suka amince su fara amfani da kuɗin Eco na bai-ɗaya.

Sai dai gwamnatin Najeriya a lokacin ta bukaci a jinkirta kaddamar da kudin na bai daya.

Tana cewa saboda akasarin ƙasashen ba su cika ka’idojin da aka gindaya ba wanda ta ce akwai bukatar a ɗage lokacin kaddamar da kuɗin.

Yanzu dai sabon shugaban ya yi maganar kuɗin a wannan lokaci wataƙila ko ya gamsu da cewa lokacin samar da kuɗin ya yi.

Zaɓen Shugaba Tinubu bai zo da mamaki ba, ganin cewa shi ne shugaban Najeriya na takwas da ya jagoranci wannan ƙungiya.

Ƙungiyar ECOWAS dai na da mambobi 15 da suka haɗa da Benin da Burkina Faso, da Cape Verde, sai kuma Gambia

Sauran su ne Ghana da Guinea da Guinea-Bissau da Ivory Coast da Liberia da Mali da Nijar da Najeriya da Senegal da Saliyo da kuma Togo. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here