Home Siyasa Shugabanci: An Shawarci Mata Da Su Yi Magana Da Murya Guda

Shugabanci: An Shawarci Mata Da Su Yi Magana Da Murya Guda

142
0
VW Turaki

An yi kira ga Kungiyoyin Mata da su hada hannu da Kungiyar Muryar Mata Mai Rajin Samar da Shugabanci na Gari wato (Voice of Women in Nigeria Leadership Initiative) wajen ganin sun bawa Kasarnan Jagoranci da za a yi alfahari das hi.

Wannan kira ya fito ne da ga bakin Shugaban Kungiyar, Hajiya Halima Turaki Tijjani a wajen Kaddamar da Shugabancin Kungiyar Karo na biyu da aka gudanar ranar Asabar a dakin Taro na Evelyn da ke Gwarinpa a birinin Taraiya Abuja.

Ta ce makasudin taron shine ya hada Kungiyoyin Mata guri guda don su rinka magana da murya daya a wani mataki na samar da Shugabanci na gari kamar yadda aka Kaddamar a Taron Beijin da ya gudana a 1995 in da aka yi bikin cika shekaru 50 wanda Majalisar Dinkin Duniya ta shirya.

Voice of Women

Hajiya Turaki ta ce, matan Najeriya sun amince su yi Magana da murya guda daya a wani mataki na baiwa kasarnan Shugabanci na gari da za a yi alfahari da shi.

Ta kara da cewa, ta na da masaniya cewa akwai kungiyoyi na mata da yawa a kasarnan amma wannan Kungiya ta Muryar Mata burin ta shi ne ta zama Muryar mata baki daya ba tare da la’akari da banbancin kungiya, Yare ko addini ba.

Har ila yau, Turaki ta ce, burin Kungiyar shi ne ta tallafawa mata ma su hazaka musamman ma su tasowa wajen basu ililmi da dabaru na kasuwanci da Shugabanci wajen ganin sun fitar da kasarnan da ga matsaloli da su ka ki ci, su ka ki, cinyewa.

Dadin da dawa, Shugaban ta ce burin su shi ne a samu dai dai to wajen samun ilimi da Shugabanci da dogara da kai da sauran bukatu na rayuwa tsakanin mata da maza ba tare da nuna wani banbanci ba.

A hira da Yan Jaridu, daya da ga cikin shugabannin Kungiyar, Hajiya Madina Dauda ta jaddada aniyar Kungiyar na ganin cewa mata sun fito an dama da su wajen ganin an samarwa da Kasarnan Shugabancin da ya kamata domin kawo cigaba mai dorewa.

VW Madina

Tace mata sun taka rawar gani a Najeriya wajen bayar da shugabanci na gari abun koyi idan aka duba irin gudunmawar da su ke bayarwa a matakai dabab-daban a Kasarnan.

Madina ta ce mata su suka fi cancanta da a mikawa ragamar shugabancin kasarnan idan akayi da la’akari da irin gaskiyar su da rikon amana da kuma bayar da tarbiya.

Daga karshe ta yi kira ga mata da maza masu kishin cigaban kasarnan das u marawa yunkurin sun a samar da shugabancin da kasarnan take bukata domin yalwatar arziki da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a kasaranan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here