Home Siyasa Shugaban Turkiyya Ya Ce Baya Shakkar Nasara A Zagaye Na Biyu Na...

Shugaban Turkiyya Ya Ce Baya Shakkar Nasara A Zagaye Na Biyu Na Zabe

180
0

Ta yiwu a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasar Turkiyya da aka gudanar a jiya Lahadi bayan da Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, wanda ya kwashe shekaru 20 yana mulkin kasar, ya kasa samun cikakkiyar nasara akan babban abokin karawarsa a zaben.

Ko za a bayyana sakamakon zaben bayan ‘yan kwanaki ko kuma bayan zagayen zaben na biyu nan da makonni biyu, zai bada tabbacin ko kawar NATOn da take tsakanin Turai da daular Larabawar za ta cigaba da kasancewa karkashin ikon Erdogan ko kuma zata dau hanyar kafa demokradiyyar da babban abokin hamayyarsa Kemal Kilicdaroglu.

Galibi zaben ya mai da hankali akan al’amuran cikin gida da suka hada da tattalin arzikin kasa, ‘yancin ‘yan kasa da batun ibtila’in girgizar kasar da ta yi sanadin mutuwar sama da mutum 5,000. Sai dai kuma, kasashen yamma da ‘yan kasashen waje masu zuba jari suna dakon sakamakon zaben domin yanayin shugabancin Erdogan na rashin sanin tabbacin tattalin arzikin kasar da kuma yunkurinsa na sanya Turkiyya tsakiyar tattaunawar kasa da kasa.

Yayin da aka kusan kammala tattara sakamakon zaben, shugaban da ke kan mulki ya rasa cikaken goyon bayan masu zaben da zai sa yayi zarra kai tsaye kamar yadda ake bukata a zaben. Erdogan ya samu kashi 46.6% na yawan kuri’un da aka kada yayin da Kilicdaroglu ya samu kasha 44.7% na kafatanin kuri’un da aka kada bisa ga alkaluman kafar yada labaran kasar, Anadolu.

Idan har babu daya daga cikin manyan ‘yan takarar biyu da ya yi zarrar samun sama da rabin kuri’un da aka kada, manyan ‘yan takarar biyu za su tafi zagaye na biyu a ranar 28 ga watan Mayu mai ci. Hukumar Zaben kasar Turkiyya (S E B), tace, tana sanar da jam’iyyun kididdigar zaben da ake yi nan take kana zata sanar da sakamakon zaben da zarar an kammala tattara sakamakon zaben.

Ana bukatar a tattara akasarin kuri’u miliyan 3.4 na ‘yan Turkiyyan da ke kasashen waje a cewar hukumar sannan babu tabbacin za a tafi zagaye na biyu.

Erdogan mai shekaru 69, ya fara shugabancin Turkiyya a matsayin Firan Minista ko kuma shugaba a shekara ta 2003. A gabanin zaben, bincike ra’ayin jamma’ar da aka gudanar ya nua cewar, shugaban mai mulkin kama karya ya baiwa abokin hammayar nashi dan tazara ne kawai.

Yayin da sakamakon zaben da ake kan tattarawa ke hasashen halin da ake ciki, ‘yan kanzagin Kilicdaroglu masu ra’ayin rikau CHP sun ki amincewa da alkaluman da Anadolu na farko, inda su ka yi zargin kafar yada labaran gwamnatin da mara wa Erdogan baya. (Muryar Amurka).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here