Home Uncategorized Shugaban Turkiyya Erdogan, Ya Soki Matakin Amurka Na Tallafawa Isra’ila Da Jirgin...

Shugaban Turkiyya Erdogan, Ya Soki Matakin Amurka Na Tallafawa Isra’ila Da Jirgin Ruwan Yaki

179
0
US War ship

A jiya Talata, shugaban Turkiyya Reccep Tayyip Erdogan ya soki matakin Amurka na tallafa wa Isra’ila da jirgin ruwan yaki da a halin yanzu ke kan hanyarsa ta isa kasar Isra’ila sannan yana mai cewa wannan mataki zai kai ga yi wa ‘yan Filasdinu kisar mummuke a Gaza.

Biyo bayan harin bazatan da ‘yan Kungiyar Filasdinu na Hamas suka kai Isra’ila a ranar Asabar, a ranar Lahadi ne Sakataren tsaron Amurka Lyod Austin ya ce, Amurka zata tallafa wa Isra’ila da jirgin yakin ta na ruwa mai rukunin makaman da su ka hada da USS R, Ford kusa da Isra’ila.

Kafar labarai ta Reuters ta ruwaito cewa, Amurka ta girke jiragen yakin ta na sama a yankin kasar Isra’ila a matsayin gargadi ga Filasdinu. “ a ranar 8 ga watan Octoba ne Austin ya bada umarnin a matsa da jirgin ruwan mai suna Gerald R. Ford kusa da Isra’ila.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here