Home Siyasa Shugaban Amurka ya aike saƙo kan zaɓen Najeriya

Shugaban Amurka ya aike saƙo kan zaɓen Najeriya

202
0

Shugaban ƙasar Amurka Joe Biden ya ce ya yaba da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka sanya wa hannu a Najeriya jiya, wadda ta haɗa jam’iyyu da ‘yan takarar da za su fafata a zaɓen shugaban ƙasar Najeriya da za a yi ranar 25 ga watan Fabirairu.

Cikin wata sanarwa da ya fitar kan zaɓen Najeriya, Shugaban Biden ya ce jam’iyyun da ‘yan takarar sun amince da cewa za su karɓi sakamakon zaben da zarar hukumar zaɓe ta ƙasar ta sanar da wanda ya ci, sannan za su taimaka wajen miƙa mulki cikin ruwan sanyi.

Sanarwar ta ce zaɓe wani ɓangare ne mai matuƙar mahimmanci a cikin tsarin dimokraɗiyya, kuma duka ‘yan Najeriya sun cancanci wannan dama ta zaɓar wanda zai shugabance su a nan gaba, cikin adalci da ruwan sanyi. “Amurka ba ta goyon bayan ko wanne ɗantakara ko jam’iyya, amma muna goyon bayan zaman lafiya da gudanar da komai a buɗe wanda hakan ya yi daidai da burin mutanen ƙasar.

“A ranar zaɓe, ina shawartar ‘yan Najeriya – ba tare da duba addini ko yanki ko ƙabilar wani ba – su fito su bayyana abin da suke so, domin haka wani ɓangare ne na ‘yancin da suke da shi – har da ƙananan yara da za su fara kaɗa ƙuri’arsu a karon farko,” in ji shugaba Biden.

Shima Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken, ya jaddadawa ‘yan Najeriya muhimmacin babban zaben da kasar za ta yi a wannan karshen makon da ke tafe.

A ranar 25 ga watan Fabrairu za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya.

Sai kuma na gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a ranar 11 ga watan Maris.

“Yayin da aka tunkari zabe a Najeriya, wannan wata dama ce ga al’umar kasar da za a saurari ra’ayinsu, ta yadda za su zabawa kasar makoma mai kyau.” Blinken ya ce a wani sakon bidiyo da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar.

Blinken ya kara da cewa, “Amurka na da matukar burin ganin an gudanar da wannan zabe cikin lumana.

“Saboda haka, kuri’arku tana da matukar muhimmanci kamar yadda wannan zabe yake da muhimmanci, ba ga Najeriya kadai ba, har ga ma sauran duniya baki daya.” In Sakataren harkokin wajen na Amurka.

Sakon bidiyion har ila yau na dauke da jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Lisa Thomas-Greenfield wacce ta ce gudanar da sahihin zabe, zai taimaka wajen tabbatuwa ko wanzuwar adalci a kasar.

Kazalika bidiyon na dauke da shugabar hukumar raya kasashe ta USAID, Samantha Powers, wacce ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su ziyarci shafin hukumar zabe ta INEC don ganin sun ilmantu kan yadda za su kada kuri’arsu.

“Amurka ta kasance babbar kawa kuma abokiyar hulda ga al’umar Najeriya.” Blinken ya jaddada. (BBC/Muryar Amurka).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here