Home Diplomasiyya Shugaba Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin Jihohin Iyakar Nijar

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin Jihohin Iyakar Nijar

280
0
Niger Boarder Governors with Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wata muhimmiyar ganawa da gwamnonin jihohin Najeriya dake da iyaka da kasar Jamhuriyar Nijar.

An gudanar da ganawa ta musamman din ne a yammacin Lahadi, 6 ga Agustan 2023 a fadar gwamnati da ke Abuja, inda Shugaba Tinubu ya gana da gwamnonin jihohin Najeriya da ke kan iyaka da Jamhuriyar Nijar.

Ganawar shugaban da gwamnonin wani bangare na tuntubar da shugaban kasar ke yi dangane da lamarin da ke faruwa a kasar Nijar na juyin mulki da sojoji suka yi a ‘yan kwanakin nan da kuma matakan kungiyar ECOWAS da shugaban Najeriya ke jagoranta.

Taron ya samu halartar manyan gwamnonin da suka hada da Gwamna Ahmed Aliyu na Sokoto, Umar Namadi na Jigawa, Mai Malam Buni na Yobe, Idris Nasir na Kebbi, da Gwamna Dr Dikko Radda na Katsina. (Muryar Amurka).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here