Home Siyasa Shugaba Buhari ya kaɗa ƙuri’arsa a Daura

Shugaba Buhari ya kaɗa ƙuri’arsa a Daura

253
0

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaɗa ƙuria’a mazaɓarsa da ke garin Daura da ke jihar Katsina.

Shugaban wanda ya fito da misalin ƙarfe 9:30 na safe ya kaɗa ƙuri’ar tasa ne tare da mai ɗakinsa A’isha Buhari.

Muhammadu Buhari na kammala wa’adin mulkinsa na shekara takwas a wannan shekara, inda ake sa rana zai miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

An samu jinkirin kai kayan zabe a wasu mazabu a Bauchi

Rahotanni daga jihar Bauchi na cewa an samu jinkirin kayan aiki a mazaɓar Madachi, a Kofar Fada da ke Ƙaramar hukumar Katagum.

A mazaɓar Shagari da ke tsakiyar Bauchi ita ma ana fuskantar wannan matsala ta rashin kai kayan aiki a kan lokaci.

Hakan abin yake a ƙofar gidan yari, kan kusurwar fada da sauran wasu wurare.

An ware wa tsofaffi da masu ciki layi na daban a Oyo

An fara kaɗa ƙuri’a a mazabar Iwo da ke Ibadan babban birnin jihar Oyo.

Tun da sanyin safiya ne masu kaɗa ƙuri’a suka isa rumfunan zaɓen domin kaɗa kuri’unsu.

Yankin na cikin inda aka fara kaɗa kuri’a a kan lokaci a kusan faɗin Najeriya, ma’ana ba su samu jinkiri ba kamar yadda aka samu a wasu wurare da dama.

Tun da fari an raba layukan masu zaɓen biyu domin sauƙaƙe komi, Layin farko na dattijai da mata masu ciki da kuma masu buƙata ta musamman.

Layi na biyu kuma matasa ne masu jini a jika da kuma lafiyayyun mutane koda suna da shekaru. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here