Home Addini Shugaba Buhari ya isa Madina

Shugaba Buhari ya isa Madina

167
0

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya isa birnin Madinah da ke Saudiyya domin soma ziyarar yini takwas.

Mai bai wa shugaba Buhari shawara kan kafafen yaɗa labarai, Mallam Garba Shehu, cikin wata sanarwa ya ce shugaban ya samu tarba daga mataimakin gwamna Sa’ud Khalid Al-Faisal.

Kakakin shugaban Najeriyar ya ce a dazu ne kuma Buhari ya kai ziyara masallacin Annabi Muhammad SAW.

Ya ƙara da cewa shugaba Buhari ya samu tarba daga wasu jami’ai a kofar shiga Masallacin Annabi Muhammad SAW.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here