Home Siyasa Shekaru 63 Da Samun Yanci: An Hori ‘Yan Najeriya Da Su Godewa...

Shekaru 63 Da Samun Yanci: An Hori ‘Yan Najeriya Da Su Godewa Allah

156
0
Hon. Yan Liman

An ja hankalin Yan Najeriya da su cigaba da godewa Allah Madaukain Sarkin akan ni’imar da ya yi wa wannan kasa ta kasance kasa daya al’umma daya a cikin shekaru 63 da su ka gabata.

Dan Majalisar Wakilai mai Wakiltar Kananan Humomin Malam Madaori da Kaugama a Majalisar Taraiya Hon. Maki Abubakar Yan Liman, ne ya  bukaci haka a hirar sa da Yan Jaridu a ofishin sa da ke Abuja.

Hon. Yan Liman ya ce idan za a kwatanta Najeriya da sauran kasashen Duniya babu wani abu da Dan Najeriya zai yi sai dai ya daga hannu ya yi wa Allah godiya domin a Aljannar Duniya muke idan muka kwatanta da sauran kasashen Duniya.

Ya ce idan aka kwatantan irin abubuwa da suke faruwa a kasarnan da sauran  kasashen duniya na sabon Allah da sauran laifuffuka kamar la’antar shugabanni toh babu abun da za a ce sai a godewa Allah.

Ya kara da cewa an samu cigaba ta fannin siyasa inda aka samu shekaru  24 a na siyasa babu tsaiko wannan babbar nasara ce ga kasarnan inji Hon. Yan Liman. Tare da nuni da cewa duk da matsi na tattalin arziki da ake ciki Yan Najeriya sun rungumi dangana ba tare da nuna bacin rai ba wanda  ya ce hakan babban nasara ce a siyasa ce.

Hon. Yan Liman babban sirrin nasarar da ya samu a mazabar sa itace sakamakon irin adduar da suke yi masa da fatan alheri na ganin ya samu nasara a dukkan aiyukan sa.

Dan Majalisar ya yi alkawarin ganin ya cigaba da jajircewa wajen ganin ya kyautatawa mutanen mazabar sa ta hanyar kawo musu aikace aikace wadanda za su inganta ruyuwar al’umar sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here