Home Addini Sheikh Shuraim ya yi ban-kwana da limancin Masallacin Makkah

Sheikh Shuraim ya yi ban-kwana da limancin Masallacin Makkah

358
0

A yanzu dai ta tabbata cewa Sheikh Saud Ash Shuraim ya bar limanci a Masallacin Ka’abah bayan da hukumar da ke kula da manyan masallatai biyu mafiya tsarki na duniya wato masallacin Makka da kuma na Madina ta fitar da jerin sunayen limaman da za su jagoranci sallar Tarawi, kuma ba sunanshi.

Tun a watan Janairu rahotanni suka bayyana cewa wani daga cikin fitattun limaman ɗaya daga cikin manyan masallatan biyu ya bar aikin.

Amma kuma sai a watan jiya na Fabarairu ta bayyana cewa limamin da zai yi ritayar shi ne Sheikh Saud Ash Shuraim.

Sai dai ba a bayyana dalilan da suka sa lilamin ya yi ritaya haka da wuri ba, amma kuma wasu kafofi sun nuna cewa shi da kansa ya buƙaci barin limancin.

Limamin wanda ya shafe shekara 32 yana jagorantar sallah, ya ja sallarsa ta ƙarshe a masallacin na Ka’abah ranar Litinin 12 ga watan Rabi Al Awwal 1443 ( Litinin 18 ga watan Oktoba 2021). (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here