Home Siyasa Shawarar da gwamnonin PDP suka yanke kan matsalolin Najeriya

Shawarar da gwamnonin PDP suka yanke kan matsalolin Najeriya

197
0
Gov Bala Bauchi

Yayin da ake ganin matsaloli na ƙara dabaibaye babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ‘ya’yan jam’iyyar na ci gaba da fadi-tashin nemo bakin zaren matsalolinsu.

Kan haka ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar hamayya ta PDP ta gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki domin tattaunawa da kuma samun matsaya kan inda jam’iyyar ke neman dosa.

Wannan ne taro na farko da ƙungiyar ta yi irin wannan taro, tun bayan zaɓen shugaban ƙasa da aka yi, kuma ya gudana ne a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

An tattauna manyan ƙalubalen da jam’iyyar take fuskanta waɗanda suka ƙi bayyana wa ‘yan jarida, suna cewa hakan bayyana lago ne ga abokan hammaya, in ji shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad.

PDP cikin abubuwan da ta tattauna, ta bukaci gwamnatin tarayya da ta ƙara himma wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar kasar.

Duk da cewa ana fama da matsalar tsaro a sassan kasar daban-daban, kungiyar ta ce lamarin ya yi muni a jihohin da PDP ke mulki.

“Mun yi la’akari da cewa abubuwa sun taɓarɓare kan maganar tsaro a jihohin PDP na Zamfara da Jihar Filato waɗanda aka rasa rayuka da dukiyar al’umma.

“Muna kira ga gwamnatin tarayya ta ɗauki mataki cikin gaggawa domin ganin shawo kan wannan taɓarɓarewar da lamura suka yi,” in ji shugaban ƙungiyar Bala Abdulkadir Muhammad.

Duk da cewa matsalar tsaron ta shafi har jihohin da jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ke jagoranci, amma ƙungiyar ta ce matsalar ta fi ƙamari a na PDP ne.

“Matsalar ta fi tsananta a jihohin Filato da Zamfara da PDP ke Mulki, A Filato an kashe mutum ya fi 300, yayin da a Zamfara ma babu wanda ya san adadin,” in ji Gwamnan na Bauchi.

Ƙungiyar ta kuma tattauna kan batun zaɓukan da ke tafe a jihohin Bayelsa da Imo da kuma Kogi wanda ta nemi a yi Hukumar Zabe ta ƙasar da ta yi adalci a yayin gudanar da su.

Gwamnonin PDPn sun yi zaman nasu ne a lokacin da uwar jam’iyyar a matakin tarayya take fama da kalubale ta fuskar shugabanci.

Tun lokacin da reshen jam’iyyar PDP na gundama ta biyar da ke karamar hukumar Andoni ya dakatar da shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa a shekara ta 2021 kujerar shugaban ta fara tangal-tangal, wadda a karshe sai da sauka daga kan mukamin, mataimakinsa ya haye kujerar a matsayin mukaddashi.

Wannan ne ya sa ‘ya’yan jam’iyyar da dama suka sa ran cewa gwamnonin jam’iyyar za su samar da mafita a wannan zaman.

Kungiyar gwamnonin PDP dai ta ce za ta yi tafiya kafada-da-kafada da jam’iyyar APC mai mulki don ciyar da kasar gaba, amma fa saboda da kaza, kamar yadda ‘yan magana kan ce ba ya hana yanka ta, kenan hakan ba zai hana gwamnonin yin hamayya ko nuna adawarsu ba idan ta kama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here