Home Siyasa Sayen Motocin Yan Majalisar Taraiya Akan Naira Miliyan 200 Zuki Tamalle Ne...

Sayen Motocin Yan Majalisar Taraiya Akan Naira Miliyan 200 Zuki Tamalle Ne Kawai – Hon. Misau

131
0
HON. MISAU

Majalisar Wakilai ta karyata  jita-jita da ake yadawa cewa za’a sayawa Yan Majalisar motoci da akai kimar su akan kudi kusan  Naira Miliyan dari biyu da cewa zuki ta malle ne kawai.

Dan Majalisar Wakilai Hon. Baffa Aliyu Misau ne ya karyata wannan batu a lokacin da ya ke hira da Yan jaridu a ofishin sa da ke             Majalisar a birnin Taraiya Abuja a ranar Laraba.

Hon. Misau ya ce daidai ne idan Yan Najeriya sun fadi ra’ayin su akan wadanda suke wakiltar su domin sune suka turo su Majalisar domin su wakilce su. Sai dai ya ce ya kamata a rinka yi musu adalci idan aka kwatanta da sauran sassa na gwamnati.

Dan Majalisar ya bayar da misali da Shugaban Kasa, in da ya ce me ya sa Yan Najeriya ba sa damuwa da yawan motocin da ake sayawa Shugaban Kasa, inda ya ce akan iya samun motoci hamsin a jerin motocin da Shugaban Kasar ya ke tafiya da su amma ba wanda ya ke magana akan su.

Ya ce Gwamnama ana saya masa motoci sama da asirin a cikin jerin gwanon motocin da ya ke tafiya da su duk lokacin da zai gudanar da wani aiki na jama’a ba tare da wani ya kalubalanci yawan motocin da su ke karkashi sa ba.

In da ya kara da cewa, shima Minista akan saya masa motoci na alfarma domin ya gudanar da aiyukan ofishin sa duk da ya ke da cewa ba zabar sa aka yi ba. Wata kila ma ba dan siyasa ba ne da ga shi sai iyalin sa.

Amma dan Majalisar Taraiya wakilin jama’ar sa ne sabo da haka shi ya fi cancanta na da ya mallaki mota mai lumfashi domin ya gudanar da aikin jama’a.

Ya ce Dan Majalisar Taraiya mota da ya kawai ake saya masa a cikin shekaru hudu domin ya yi amfani da ita wajen gudanar da aikin ofishin da ya ke wakilta.

Hon. Misau ya ce ya kamata Yan Najeriya su rinka yi musu adalci idan aka kwatanta da yawan motocin  da ake sayawa Shugaban kasa da Gwamnoni da Ministoci.

“ so ake mu rinka ya wo a kafa? Wadannan motoci na aiki ne domin mu zaga kasarnan mu ga yadda al’amura su ke domin muyi dokoki da za su amfani Yan Najeriya baki daya”.

Har ila yau, ya ce motocin da ake magana akan su farashin su ya na samuwa ne sakamakon farashin dalar Amurka wacce a halin yanzu ta kai sama da  Naira Duba akan kowacce Dala sabo da haka Yan Kwangila da ake bawa damar su sayo ba zaiyiwu su fadi ba – dole su ci riba.

A wani bangaren kuma Dan Majalisar ya kalubalanci Babban bankin Najeriya akan da ge takumkumi da ya yiwa wasu kayayyaki da ga ciki harda tsinken sakace baki da wilbarrow da karafunan rufi da Shinkafa da sauran su.

Ya ce wannan abun kunya ne a maimakon a karfafawa kamfanoni na gida domin su samar da wadannan abubuwa sai aka cire takumkumi wanda zai bawa wasu kasashe dama su samar da aiyukan yi ga al’umarsu a yayin da mu kuma muke kashe namu masana’antun.

Hon. Misau ya ce ya ya za’ayi da namu masana’antu da aka fara samarwa da su ke sarrafa shinkafa misali. In da ya ce kamata ya yi a inganta su ba a rufe su ba. Ya kara bayar da misali da kamfanin sarrafa karafa na Ajakuta wanda aka banzatar das u shekara da shekaru.

Dan Majalisar ya ja hankalin Yan Najeriya da ce wa dole mu gayawa kan mu gaskiya in har muna so mu cigaba. “A yadda mu ke tafiya a halin yanzu ba da gaske mu ke ba” inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here