Home Siyasa Sarautar Kano: Yayin Da Jami’an Tsaro Na Musamman Daga Abuja Ke...

Sarautar Kano: Yayin Da Jami’an Tsaro Na Musamman Daga Abuja Ke Gadin Sarki Bayero, Yan Farauta Ne Ke Gardin Sarki Sanusi

181
0
Sunusi Bayero

A cigaba da yamutsin sarautar Kano da ake ta fama da shi inda sarakuna biyu kowa ke sarauta a Kano lamarin sai kara ƙazanta ya ke yi.

Sarki Aminu Ado da yake fadar Nasarawa, na samun tsaro ta musamman ne daga jami’an tsaro da aka turo su daga Abuja, shi ko, Sarki Sanusi da yake faradar rumfa, na samun kariya ce daga ƴan banga da mafarauta da ke kare shi.

Wannan yamutsi na sarautar Kano ta ɗaiɗaita sarautar mai ɗinbin tarihi inda a Karon farko an samu sarauta mai asali irin haka da sarakai biyu, kowa na zuba mulki a fadarsa.

Su kan su hakiman jihar sun rabu biyu, wasu na ɓangaren sarki Aminu Ado, wasu kuma na tare da Sarki Muhammadu Sanusi. Duk da haka akwai waɗanda su kuma suna tsakiya ne ba su nan ba su can.

Dukkan su sarakunan biyu sun ja daga, ba bu wanda yake so ya hakura wa wani. Lamarin da ya sa sarautar Kanon ta fara ficewa mutane da dama a rai.

A cikin makon gobe ne ake sa ran kotu za ta fara sauraren karar da aka shigar kan rikicin sarautar Kano ɗin. (Premium Times Hausa).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here