Home Siyasa Sanatocin Arewa Sun Bukaci Tinubu Da Ya Cire Takunkumin Da Aka Sanyawa...

Sanatocin Arewa Sun Bukaci Tinubu Da Ya Cire Takunkumin Da Aka Sanyawa Nijar

69
0
IMG 20231017 WA0051

Kungiyar Sanatocin Arewacin Nigaria, sun yi Allah wadai da yawan juyin mulkin da ake yi a kasashen Nahiyar Africa ta yamma tare da neman shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu na dage takunkumin da ya sanya a kan iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Niger sakamakon juyin mulkin

Taron ya cimma wannan matsaya ne bayan kammala tattaunawa kan batutuwan daban daban daga cikinsu har da juyin mulkin jamhuriyar ta Niger da matsalolin da suka biyo baya.

Da yake zantawa da.manema.labarai bayan.kammala taron sanatocin shugaban kungiyar santa Abdul Ahmad Ningi, ya bayyana karara cewa sun yi Allah wa dai da yawan juyin.mulkin da ake yi a.nahiyar ta Africa ta Yamma, musamman ma yaduwar alamarin ga kasashen dake kan tsarin Dumukradiyya

Ya ce.musamman.ma juyin.mulkin makwabciyar Najeriya wato jamhuriyar Niger, inda taron ya roki sojawan.Niger din su.kaunaci Allah wajen sassauta matsayinsu tare da baiwa shugaba Bazum damar zabar kasar da yake son zama shi da iylansa ko me syka hango na yin wannan kira a yanzu sanata Abdulrahman Kawu Sumaila ya yi karin haske dangane da taron kamar haka.

kungiyar ta bukaci shugaban.gamayyar kasashen Nahiyar Afirka ta yamma ECOWAS Bola Ahmad Tinubu ya sassauta tare da duba dangantakar kasashen biyu a can baya lokacin yakin basasar Nigeria kamar yadda sanata Abdul Ningin ya ce.

Sanatan ya ce babu shakka mun jima hade da juna ta fuskoki daban daban kama daga al’adu dangantakar jini da zumuncin auratayya, asali da kasuwanci yanuwartakar juna sannan a lokacin yakin basasa sun mara mana baya bai.kamata a manta da wannan ba

Baya ga wannan ta bakin sanata Abdul.Nigi kungiyar sanatocin na arewacin Najeriya ta ja hankalin sojojin na Niger su hanzarta fidda jadawalin sake kafa wata gwamnatin zababbun wakilan jamaa ta fuskar tsarin Dumukradiyya ba tare da Jan kafa ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here