Home Diplomasiyya Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Ya Tattauna Da Tinubu

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Ya Tattauna Da Tinubu

186
0

A ranar 29 ga wannan wata na Mayu za a rantsar da Tinubu wanda ya lashe zaben da aka yi a watan Fabrairu.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken ya tattauna da zababben Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ta wayar tarho.

Wata sanarwa da kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Matthew Miller ya fitar a shafin yanar gizon ma’aikatar a ranar Talata, ta ce tattaunawar da suka yi, ta karkata ne kan yadda Amurka da Najeriya za su kara yaukaka dangantakarsu.

“Sakataren harkokin wajen Amurka Antony J. Blinken ya gana da zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a wannan Safiya (Talata) don ya kara nuna shirin Amurka na ci gaba da karfafa dangantakarta da gwamnatin Najeriya mai jiran gado.

“Sakataren ya bayyana cewa, an gina kawancen kasashen biyu ne kan wasu muradu da suke girmamawa da kuma kyakkyawar alaka da ke tsakanin jama’ar kasashen biyu, kuma akwai bukatar wannan alaka ta dore karkashin gwamnatin zababben Shugaban kasa Tinubu.” Sanarwar ta Miller ta ce.

A cewar Miller, Blinken da Tinubu sun kuma tattauna kan muhimmancin shugabancin da zai dama da daukacin ‘yan Najeriya, hadin kai a fannin tsaro da samar da sauye-sauye don tallafawa fannin tattalin arziki.

A ranar 29 ga wannan wata na Mayu za a rantsar da Tinubu wanda ya lashe zaben da aka yi a watan Fabrairu.

Bangaren jam’iyyun adawa na kalubalantar sakamakon zaben a kotu. (Muryar Amurka).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here