Home Siyasa Sabon Shugabancin Kungiyar NASSLAF Ya Sha Alwashin Magance Matsalolin Yan Kungiyar

Sabon Shugabancin Kungiyar NASSLAF Ya Sha Alwashin Magance Matsalolin Yan Kungiyar

114
0
IMG 20240315 130315

Sabon Shugabanci na Kungiyar Mataimaka ña Yan Majalisar Taraiya (NASSLAF) ya sha alwashin ganin ya magance dukkan matsalolin Kungiyar ta hanyar tuntubar dukkan bangarorì a wani mataki na kawo karshen tirka-tirka da ta addabi kungiyar shekara da shekaru.

Mataimakin Shugaban Kungiyar Hon. Isyaku Baba Sale ne ya tabbatar da haka a hirar sa da Jaridar Viewfinder,  jimkadan da kaddamar da sabon Shugabanci na Kungiyar da ya gudana a ranar Juma’a a wani zaure na Majalisar Datttawa.
Hon. Sale ya ce tun lakacin da su ke yakin  neman  zabe sun yi duba akan dumbin matsaloli da su ke addabar Yan Kungiyar wadanda su ka hada da rashin biyan su albashi akan lokaci da alawus-alawus da kuma rashin samun cikakken horo wajen gudanar da aiyukan su.
Ya ce Kungiyar tuni ta fara tuntubar masu ruwa da tsaki akan harkar Majalisar wajen ganin an warware dukkan matsalolin da su ke addabar Kungiyar.
Mataimakin Shugaban ya kara da cewa Kungiyar ta yi sa’a cewa Shugaban Majalisar Dattawa,  Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Wakilan,  Tajudeen Abbas da Kuma Magatakaddar Majalisar wato Clerk (CNA) su na da kunnen sauraro kuma a shirye su ke su warware matsalolin Kungiyar.
Hon. Sale ya kara da cewa tuni an saka a cikin kasafin kudi na shekara ta 2024 wasu daga cikin bukatun Kungiyar.
Da ga karshe ya yi kira ga abokan adawar su da su zo su hada hannun wajen ganin an ciyar da Kungiyar gaba ta hanyar bayar da shawarwari da kuma gabatar da manufofin su ga shugabancin Kungiyar don a saka su a cikin jadawalin gudanar da kungiyar.
Tun da fari, Shugaban Kungiyar Barista Emeka Nwala a cikin jawabin sa ya sha alwashin samar da Shugabanci na gari ta hanyar tuntubar dukkannin masu ruwa da tsaki na Kungiyar domin a gudu tare a tsira tare.
Nyala ya yi alkawarin ganin cewa a na biyan mambobin Kungiyar hakkokin su akan lokaci. Musamman albashi za a rinka biyan su 25 na kowanne wata kamar  yadda a ke biyan Ma’aikatan Majalisar.
Bayan haka ya yi alkawarin ganin an biya hadiman hakkin su na kwanakin aiki 28. Tare da ganin ya fito da wani tsari na ganin mambobin Kungiyar sun mallaki gidaje na kan su a Abuja a cikin shekaru 4 da za su yi.
Dadin dadawa, Barrister Nwala ya yi kira ga Shugabanci na Majalisar Taraiya da su tallafawa Kungiyar da motocin Zirga-zirga guda 6 don saka su akan titunan Abuja a wani mataki na rage mu su radadi na rayuwa da a ke fama da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here