Home Siyasa Sabon Shugaban Kwamitin Soji Na Majalisar Wakilai Ya Sha Alwashin Hada Kan...

Sabon Shugaban Kwamitin Soji Na Majalisar Wakilai Ya Sha Alwashin Hada Kan Rundunonin Tsaro Su Yi Aiki Tare

168
0
HON. Balele 3

Sabon Shugaban Kwamitin Sojoji na Majalisar Wakilai Hon. Aminu Balele ya sha alwashin ganin cewa duka bangarorin rundunonin Tsaro na Kasa sun yi aiki tare ta yadda za a maganta matsalar Tsaro da ta addabi Yankin Arewa da ma Najeriya baki daya.

Dan Majalisar mai Wakiltar kananan Hukumomin Dutsin-ma da Kurfi daga Jihar Katsaina a Majalisar Taraiya ya sha wannan alwashi ne a lokacin da ya ke ganawa da Yanjaridu a ofishin sa da ke  Majalisar a jiya Talata.

Hon. Balele wanda shi ne Tshohon Shugaban Kwamitin Ma’aikatar Gidaje ya ce zai yi amfani da shawarar masana wajen ganin an dinke baraka da ke tsakanin hukumomin Tsaro wajen ganin an sami sauyi ta yadda za a magance matsalar Tsaro da ta addabi Yankin Arewa maso Yamma da Jihar sa ta Katsina da ma Najeriya baki daya.

Ya ce irin tsare – tsare da ya fito da su lokacin da ya ke Shugaban Kwamitin Gidaje wadanda su ka tallafawa Ma’akatar wajen samun nasarori da su ka haifar da gina gidaje ma su dubbin yawa ga Yan Najeriya zai fito da wasu dabaru da za su tallafawa jam’an Tsaro wajen magance ta’addanci da ya ki ci yaki cinyewa a Kasarnan.

Balele ya ce yana da kyakkyawar alaka da manyan tsoffin jami’an Tsaro wadanda zai yi amfani da shawarwarin su wajen ganin ya fito da wani tsari da zai tallafawa rundunar Sojojin da ma sauran hukumomin tsaro na magance matsalar Tsaro da ta addabi Kasarnan.

Dan Majalisar ya yabawa  Kakakin Majalisar Wakilai , Tajuddeen Abas da ya ga dacewar sa ya nada shi a matsayin Shugaban Kwamitin Sojajin bayan a da ya nadashi Shugaban Kwamitin Gidaje du ka a cikin shekara guda duk da yake cewa wannan shi ne karonsa na farko a Majalisar. In da ya yi alkawarin ganin cewa ba zai ba shi kunya ba kamar yadda bai ba shi ba lokacin da ya ke shugabantar Kwamitin Gidaje.

A daya bangaren kuma ya jinjinawa Gwamnan sa na Katsina Dikko Radda, wanda ya ce irin matakai da ya ke dauka na magance matsalar Tsaro a Jihar Katsina abun a yaba ne domin ya nuna irin kishi da jajircewa da Gwamnan ya ke da shi na ganin an kawo karshen ta’addanci a jihar. In da ya ce shima zai yi shawara da shi da sauran kwararrun jami’an tsaro da su ke Jihar don kawowa Najeriya mafita na matsalar Tsaro da ta addabe ta.

A yayin da ya ke baiyana ra’ayin sa akan batum Najeriya da ta cika shekaru 25 ta na gudanar da mulkin Demokradiyya cewa ya yi kwalliya ta biya kudin sabulu domin shafe wadannan shekaru ya nuna cewa Demokradiyya ta na samun zama da gindin ta.

Hakan ya ce ya bawa Yan Kasa dama na su zabi wadanda su ke so su jagorance a matakai daban-daban ba tare da la’akari da bambancin Jam’iya ba musamman idan aka kwatanta da wannan Majalisa ta goma da ta samar da Wakilai da ga jam’iyu dabam-dabam irin su SDP da APGA da LP da APC da PDP da sauran su ya ce, wannan ba karamin cigaba bane.

Bayan haka ya ce mutane su na da yancin fadin albarkacin bakin su bs tare da wata cuzgunawa ba sabanin lokacin mulkin Sojoji. Har ila yau, ya baiyana irin nasarori da aka samu a bangarori irin su  tituna da yalwatar jami’o’I da asibitoci da sauran kayan more rayuwa duka a karkashin mulkin Demokradiyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here