Home Uncategorized Sabo Taken Najeriya: Manufar Sa Ya Zaburar Da Yan Kasa Su Gina...

Sabo Taken Najeriya: Manufar Sa Ya Zaburar Da Yan Kasa Su Gina Kasar Su – In ji Shugaban Kasa, Majalisar Taraiya

67
0
PBAT AT NASS SINGING NATIONAL ANTHEM

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu y ace dalilin canza Taken Najeriya shi ne don ya zaburar da Yan Najeriya su zama masu kishin Kasa wanda hakan ne zai basu kwarin gwiwa wajen gina Kasarnan da kuma yakar duk wani abu da ka’iya kawo nakasu wajen cigaban ta.

 

Shugaban kasar ya fadi haka ne a yayin da ya kaddamar da sabon Taken Najeriya a wani zama na musamman day a yin a Hadaka da Yan Majalisar Dattawa da ta Wakilai wajen bikin cika shekara daya da yayi akan mulki da kuma cika shekaru 25 da aka gudanar ana mulkin Demokradiyya babu kakkaukawa.

 

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio wanda ya jagoranci zaman na Hadaka, bayan ya yiwa shugaban Kasar maraba da zuwa, ya bawa shugaban Kasar zabi na yayi jawabi ko kuma ya yi shiru abun sa a dan takaitaccen zaman.

 

Akpabio y ace makasudin wannan zama shi ne don a kaddamar da sabon Taken Najeriya ne kuma a kaddamar da wani sabon Dakin Karatu na zamani da Majalisar ta Kammala ginawa a wani mataki na adana bayanai da yin bincike akan aiyukan Majalisar.

 

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya ce ziyarar ta sa ya kawo ta ne domin nu na girmamawa da ya ke yiwa Majalisar Taraiya kuma yana taya su murnar cika shekaru 25 ana gudanar da siyasa a Kasarnan ba bu yankewa .

 

Shugaba Kasa Tinubu  ya shawarci yan Majalisar da ma Yan Najeriya cewa ba bu wani da ya fi cancantar ya gina Kasarnan kamar Yan Najeriya da kansu.

 

Tinubu ya yabawa Yan Majalisar Taraiya da su ka amince da wannan sabon taken Najeriya wanda burin sa shine ya bawa Yan Kasa  kwarin gwiwa wajen gina Kasar su.

 

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu da Yan Majalisar Taraiyar sun kaddamar da sabon Taken Najeriya ta hanyar rera shi a tare.

 

Babban sakon Shugaban Kasar shi ne ya ja hankalin Yan Najeriya da su saka kishin Kasa wajen gina Kasarnan cewa ba wani da zai zo da ga wata Kasa ya gina mana Kasarnan.

 

Kakakin Majalisar Wakilan, Tajudeen  Abbas a jawabin sa ya yabawa Shugaban Kasar    irin wannan kishin Kasa da ya ke nunawa wajen gina Kasarnan a in da ya ce Majalisar Taraiya a shirye take ta yi aiki tare da Shugaban kasar.

 

Bayan da Shugaban kasar ya Kaddamar da Taken Najeriya ya kuma bude sabon dakin karatu wanda Majalisa ta 9 ta gina.  Dakin karatun na zamani ni ne wanda zai bawa Majalisar dama ta rinka adana bayanai akan aiyukan Majalisar da kuma yin bincike.

 

Sai kuma Shugaban Kasar da tawagar sa ta re da Yan Majalisar su ka dunguma domin kaddamar da jirgin Kasa wanda Gwamnatin Muhammadu Buhari ta samar a wani mataki na inganta shi da kuma cigaba da amfani da shi.

Sen. Kawu 2

Sanatan Kawu Sumaila cewa yayi wannan  ziyara ta Shugaban Kasa ta nuna irin kyakkyawan alaka da  ke tsakanin Fadar Shugaban Kasa da Majalisar Taraiya.

 

Ya ce a cikin shekaru 25 da Najeriya ta shafe ta na mulkin Demokraadiyya an samu nasarori da kalu- bale masu yawa. In da ya ce kalubalen sun faru ne sakaumakon matsaloli da suka taru shekara da shekaru.

 

Sanata Kawu  ya ce wannan sabuwar Taken Najeriya da Shugaban kasar ya kaddamar wani mataki ne na kwarara gwiwar Yan Najeriya wajen nu na kishin Kasa wanda a ke bukatar a sa shi a zuciya, a furta, sannan kuma a aiwatar.

 

Shi kuma Sanata SimYon Lalong wanda shi ne jagoran yakin neman zaben da ya kawo Gwamnatin Tinubu cewa ya yi wannan sabon taken Najeriya na da ga cikin abubuwa da su ke ckin kudurin Shugaban kasar.

.

Ya ce sabon taken zai tsuma Yan Najeriya wajen bunkasa Kasa kamar yadda wasan Kwallon Kafa ya ke hada kan Yan Najeriya a yayin da ake gudanar da wani wasa da Najeriya da wata Kasa ta Duniya.

 

Shima Hon. Ado Alasan Doguwa, Sardaunan Rano ya yabawa Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu sabo da umarnin da ya bawa Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Sharia umarnin shigar da karar Gwamnoni a Kotu kan batum cin gashin kai na kananan Hukumomi.

Hon. Doguwa Sardauna

Hakan ya ce zai kawo cigaban tattalin arzikin mutanen kananan Hukumomin da kuma magance matsalar tsaro da ta addabi kasarnan musamman Yankin Arewacin Kasarnan.

 

Ya ce kalubalen da ake fuskanta a Kasarnan su na da alaka da matsaloli da suka dabaibaye tsarin gudanar na ma’aikatun Gwamnati wanda ya ce su na da alaka da rashin kishin kasa.

 

Sabo da haka y ace Sabon Taken Najeriyar zai yiwa Yan Najeriya matashiya akan abubuwan da ya kama su rinka yi da wandan da bai kamata su yi ba a lokacin das u ke ma’amala da junan su da gudanar da mulkin Kasarnan.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here