Home Mulki Sabbin Ministoci: Yadda Suka Kama Aiki Bayan An Rantsar Da Su

Sabbin Ministoci: Yadda Suka Kama Aiki Bayan An Rantsar Da Su

162
0
Min. Dangiwa in office

Bayan da Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya rantsar da sabbin Ministocin sa guda 45 kusan dukkannin su sun runtuma ne zuwa ma’aikatu da aka basu domin su gudanar da aiki. A yayin da masoyan su da yan uwansu suka yi cincirindo a ofisoshin su da gidajen su domin su taya su murna na wannan mukamin da suka samu.

A yayin da birnin taraiya Abuja ya dauki wani yanayi da aka shafe watanni an ji shiru na irin jiniya da ta saba mamaye birinin; kukan jiniya kakeji ko ta ina, in bakayi bani wuri.

Guraren taruka kuwa kusan dukkan su sun cika makil da mutane domin karrama wadannan Ministoci. Jaridar Viewfinder ta samu halartar wasu daga cikin wadannan guraren taron domin ta kawo muku irin wainar da aka toya awadannan wurare.

A wurin taro na ‘A Class’ dake Maitama, ministoci uku ne wadanda su ka hada da Arc. Ahmed Dangiwa, da Bar. Festus Keyamo da kuma Ministan dake wakiltar Jihar Neja ne suka sha biki a wannan gurin taron.

A cikin jawabin sa Ministan Gidaje da Muhalli, Arc. Dangiwa ya nuna farincikin sa da wannan mukami da ya samu tare da yin alkawarin ganin be baiwa Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu da Yan Najeriya kunya ba.

Ya ce, mukamin da aka bashi dama abun da ya karanta kenan kuma shine abun da ya ke yi shekara da shekaru; inda ya ce zai yi amfani da dukkan basirar sa wajen ganin ya kawo gagarumin cigaban a fannnin da aka dora shi.

Arc. Dangiwa ya ce akwai karancin gidaje a Najeriya kuma Yan Najeriya suna bukatar gidaje masu kyau kuma masu sauki; sabo da haka zaiyi kokari wajen ganin ya samar da gidaje da  za’ayi alfahari da su kamar yadda ya yi lokacin da ya jagoranci bankin “Mortgage”.

Hon. Aminu Balele da ga Jihar Katsina ya ce nada Arc. Dangiwa a matsayin Ministan Gidaje da Muhalli ya yi daidai da abun da Hausawa ke cewa an dora Kwarya a gurbinta.

Balele ya yi wa Yan Najeriya albishir cewa za su ga kyakkyawan shugabanci domin kuwa ya tabayi an gani kuma zai ci gaba da abun da ya kware akansa. Sabo da haka , ya nemi Yan Najeriya da su yiwa Dangiwa addu’a Allah ya bashi ikon sauke nauyin da ya dauka.

Shima Tsohon Sanata, Emmauel Bwacha da ga Jihar Taraba ya taya Ministansa murna tare da yi masa fatan alheri. Inda ya nemi Yan Najeriya da su taya shi da addu’a da kuma yin hakuri na halin da suke ciki; inda ya yi albishir da cewa za a samu sauki nan ba da dadewa ba.

A daya bangaren kuma daura da wurin taro na ‘A Class’, Ministocin Jihar Kano ne suka gwangwajen na su bikin. Wurin taron na Jihar Kano ya samu halartar Karamin Ministan Gidaje da Muhalli, Hon. Abdullahi Tijjani Muhd Gwarzo, da Hon. Mariya Bunkure, Karamar Ministan Birnin Taraiya Abuja da Shugaban Jam’iyar APC na Kasa, Dr. Abdullahi  Ganduje da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da sauran masu fada aji a Jihar Kano na Jam’iyar APC.

Mins. Ganduje

A jawabinsu Ministocin, sun nana farin cikin su da samun wannan mukami da yin alkawarin cewa ba za su bawa Jihar Kano da Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu da Yan Najeriya kunya ba wajen ganin sun sauke nauyin da ya ke kansu. Inda suka nemi addu’ar mutane wajen ganin sun sami nasara akan wannan aiki.

Anasa jawabin, Shugaban Jam’iyar APC na Kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa Ministocin guda biyu na irin juriya da aiki tukuru da sukayi lokacin da suna mulki a Jihar Kano wanda ya ce hakanne ya sa aka ga cancantarsu wajen basu wannan mukami na Minista.

A yayin da ya ya ce, A.T.M Gwarzo ya cika mutum mai hakuri, inda ya bada labarin yadda sau uku yana bashi hakuri akan bukatarsa ta neman Sanata kuma ya hakura. Inda ya ce, wannan hakuri ne ya haifar masa da wannan mukami na Minista.

Ganduje, ya ce, ita kuma Mariya Bukure ta sami wannan mukami ne sakamakon irin kokarin da ta yi lokacin da tana Kwamishinan Ilimi mai Zurfi a Jihar Kano wanda ya haifar da Karin Jami’a a jihar.

Bayan haka, ya ce lokacin da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya ba shi minti goma da ya kawo mace guda daya da za’a yiwa Minista sai Ganduje yace “ abun da ya zomin rai shine Gwaggo, sai na kira ta na ce da ita, kinji abun da shugaban kasa ya ce, sai tace, ba ga Mariya Bunkure ba, me ake da bukata. Sai na ce da Shugaban Kasa, an samu. Sai ya ce da ni ‘Is she honest? I said, Yes sir, Is she hardworking? Sai na ce Yes sir. Sai Shugaban Kasa ya ce: Ganduje! Ganduje!! Ganduje!!!”

Mins. Barau and co

Dukkan tarurrukan da aka gudanar a Abuja an ci an sha kuma an nishadantu daga makida da mawaka irin daban daban

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here