Home Cinikaiyar Zamani Ruga: Tsugunar Da Fulani Guri Guda Ba Zai Yiwu Ba A Najeriya...

Ruga: Tsugunar Da Fulani Guri Guda Ba Zai Yiwu Ba A Najeriya – In Ji Tsohon Shugaban Miyetti Allah

72
0
herds of Cattle

An baiyana yunkuri da Majalisar Taraiya ta ke yi na yin Doka da za ta tsugunar da Fulani a wuri guda ta hanyar samar da Ruggage a sassan Kasarnan wani mataki da zai yi wuyar aiwatarwa a Najeriya.

Tsohon Shugaban Meyetti Allah na Babban Birnin Taraiya Abuja, Muhammadu Dodo Oroji ne ya sanar da haka a hirar sa da Yan jaridu da ya gudana a Abuja a satin da ya gabata.

Ya ce Najeriya bata da wadatattun filaye da za ta mallakwa Fulani wanda zai ishe su, su killace shanun su a guri guda. Dadin dadawa ma, Najeriya ba ta da kyakkyawan yanayi da ake bukata na kiwo sabo da canji na yanayi da ake samu na rani da damina.

Oroji ya bayar da misali da Kasashen Amurka da Holand da Brazil in da ya ce akwai makiyaya da su ke da gona mai fadin murabbu’I kilomita hamsin 50 ta yadda makiyayi zai iya ware gurare na shuka ciyawa domin shanun sa su yi kiwo kuma ya na juya su zuwa wani bangare a lokaci zuwa lokaci.

Ya ce a Najeriya akwai makiyaya dubunnai da su ka mallaki shanu da ga 1000 zuwa sama da 5000 wanda zai yi wuya a iya killace su a wuri guda kuma a sama mu su abincin da su ke bukata.

Oroji ya kara da cewa, mafita ita ce ya kamata Yan Najeriya su fahimta cewa Bafulatani shi ma dan Najeriya ne kuma ya na da yancin ya je duk in da ya ke so domin ya gudanar da kasuwancin sa kamar yadda ake kyale wasu kabilu su je duk in da su ke so su yi sana’ar su irin ta sayar da kayan mota da magunguna da sauran su.

Tshohon Shugaban ya ce abu mafi mahimmanci shi ne a kyale kowa ya yi sana’ar sa a bisa doron doka da oda ba tare da wata musgunawa ba. Kuma gwamnati ta hukunta duk wanda ya karya dokar Kasa ko shi wanene ba tare da la’akari da bangaranci ko kabila ba.

Oroji

Ya ce Fulani yan kasuwa ne kamar kowa kuma sun yi daruruwan shekaru su na gudanar da kasuwancin su na kiwo a Kasarnan da ma wasu kasashen makota. Sabo da haka idan sun karya dokar Kasa ko kuma sun ci kayan abincin gonar wani mutum to ya zama wajibi a hukunta duk Bafulatani da ya yi hakan kamar yadda ya rinka yi a matsayin sa na shugaban Fulani a birinin Taraiya Abuja shekaru asirin da su ka wuce.

“Idan Bafulatani ya ci doyar Gwari a Abuja a waccan lokacin abun da na rinka yi shi ne zan kirawa Bafulatanin da Gwari na tambaye shi doyar sat a nawa ce? Balatanin ya biya shi. Kuma an zauna lafiya” in ji shi.

Shugaban ya nu na irin mahimmancin da Fulani su ke da shi a Kasarnan, in da ya ce Najeriya bata shi go da nama da ga wata Kasa, Fulani ne su ke samar da naman da ake bukata a Kasarnan. Bayan haka su na samawa kasarnan kudaden shiga na biliyoyin nairori ta hanyar nama da kashi da kaho da nono da sauran su.

Amma  ya ce, duk da irin wadannan abubuw das u ke samarwa a Kasarnan ba wanda ake zalunta kamar Bafulatani ta hanyar  kashe su da kwace mu su shanun su; har wani lokacin ma a yi lalata da iyalin sa amma gwamnati ba a bun da ta ke yi akan hakan.

Ya kara da cewa, a bangaren tallafi gwamnati ba ta tallafawa makiyaya ta kowacce hanya duk da irin gudunmawar da su ke bayarwa ta fannin tattalin arzikin Kasa; amma ta na tallafawa manoma da taki da iri kai harma da wasu kayan noma.

Oroji ya shawarci gwamnatoci da Majalisar Taraiya da su samar da Doka da zata kare hakkin Makiyaya kamar yadda aka kare ta masu sayar da Taya da magani su ma a samar mu su da filayen kiwo da burtali domin su gudanar da kasuwancin su ba tare da wata tsangwama ba.

Ya ce, hakkin gwamnati ne ta kare rayuka da dokiyoyin al’umma kuma Fulani ma Yan Najeriya ne kamar kowa sabo da haka dole a kare mutumcin su da dukiyar su domin a zauna lafiya a Kasarnan.

Ya bukaci gwamnatoci da su rika tallafawa Fulani da sama mu su ilimi irin na “nomadic education” kamar yadda ake yi a baya wanda hakan ya haifar da manyan yan boko a fannoni daban-daban tare da ba su ilimin kiwo na zama ni wanda zai bunkasa sana’ar su ta kiwo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here