Home Cinikaiyar Zamani Rikicin Masarautar Kano: Za Mu Bi Umarnin Kotu – Kwamishinan Yansandan Jihar...

Rikicin Masarautar Kano: Za Mu Bi Umarnin Kotu – Kwamishinan Yansandan Jihar Kano

155
0
IMG 20240105 WA0001

Jami’an tsaro a Kano sun ce sun karbi umarnin kotu kuma za su yi amfani da shi tare da samar da cikakken tsaro a faɗin jihar Kano.

Cikin wani jawabin hadin gwiwa da jami’an tsaron suka gabatar wa manema labarai a shalkwatar ‘yan sanda da ke Bompai, kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Usaini Gumel ya ce jami’an tsaron suna biyayya ne da umarnin da kotun tarayyar da ke Kano ta bayar.

Kotun tarayyar dai ta bayar da umarnin dakatar da soke masarautun jihar bayan shigar mata da ƙorafi kan hakan, sannan ta saka ranar 3 ga watan Yuni domin fara sauraron ƙasar.

Don haka CP Gumel ya ce jami’an ‘yan sanda tare da haɗin gwiwar sojoji da sauran jami’an tsaro za su yi aiki tare domin samar da cikakken tsaro kamar yadda kundin tsarin Najeriya ya tanadar.

Kwamishinan ‘yan sandan ya kuma yi kira ga mazauna birnin Kano da su kwantar da hankula tare da bai wa jami’an tsaro hadin kai, musamman yadda ya ce an san al’ummar jihar wajen bin doka da oda, kafin kotu ta yanke hukunci kan batun ranar 3 ga watan Yuni.

CP Usaini Gumel ya kuma gargaɗi duk wanda ya yi yunƙurin karya doka a jihar da cewa zai fuskanci fushin jami’an tsaro.

Yana mai cewa jami’an tsaron sun baza komarsu a faɗin birnin domin tabbatar da zaman lafiya da bin doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here