Home Diplomasiyya Rikicin Gaza: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Gwamnatin Najeriya Da Majalisar Dinkin Duniya...

Rikicin Gaza: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Gwamnatin Najeriya Da Majalisar Dinkin Duniya Su Dakatar Da Zubar Da Jini Haka

66
0
SEN. Kawu

Majalisar Dattijan Najerya ta buƙaci gwamnatin ƙasar ta haɗa kai da Majalisar Dinkin Duniya (MDD) domin ganin an tsagaita wuta a hare-haren da Isra’ila ke kai wa zirin Gaza wanda ya yi sanadiyyar a sarar ruyuka masu yawa.

A wani kudiri da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaaila daga Jihar Kano ya tsara, aka kuma gabatar da shi jiya Talata a gaban majalisar bayan zazzafar muhawara, dukkanin yan Majalisar bakin su ya haɗu wajen neman Najeriya ta bayyana matsayarta a rikicin na Gaza.

Majalisar Dattawar ta bayyana mace-mace da kuma adadin waɗanda suka rasa muhallansu sakamakon rikicin na Isra’ila da Hamas a matsayin abin tsoro.

A tattaunawarsa da yan Jaridu Sanata Kawu Sumaila ya ce sun yi la’akari da abubuwan da suke faruwa sun kai maƙura da ya kamata Najeriya ta bayyana matsayarta kan wannan rikici.

“Kamar bai kamata ba idan aka yi la’akari da da matsayinmu a duniya da kuma Afrika a ce mun naɗe hannu mun yi shiru.

“Shi yasa muka haɗu muka zo da wannan kuɗuri ga ita gwamnatin Najeriya domin ta haɗa hannu da MDD wajen ganin an kawo ƙarshen wannan abu da ke faruwa,” in ji Kawu Sumaila.

Sanatan ya ce buƙatar Majalisar ta biyu ita ce ta nuna goyon bayan bai wa ko wanne ɓangare tsakanin (Isra’ila da Falasdinu) gashin kansa.

“Menene abin da mutane da suka zaɓe ni ke nuna damuwa a kai, ko hankalinsu yake kai. Na ga tunanin mutane da damuwar da suke nuna yadda ran ɗan adam ya koma kamar ba na ɗan dama ba.

“Yadda ake karya dokokin yaƙi da mutuntaka ta ƙasa da ƙasa, dole mu yi magana,” in ji Sanatan.

Ita ƙasa ba zaman kanta take yi ba zaman al’umma take in shi, kuma idan ta bauɗe sai muja hankalinta a matsayinmu na wakilan ƙasa.

Wakilin BBC ya tambayi sanatan kan cewa ba sa ganin matakin da suka ɗauka zai iya shafar dangantakar Najeriya da Isra’ila, musamman inda take cewa babu batun tsagaita wuta har sai an sako mutanenta da aka yi garkuwa da su?

Sai Kawu Sulamaila ya ce, “abin ba iya Najeriya ba ne, Afrika ta Kdu da Shugabanta sun tsaya sun bayyana matsayarsu a fili. MDD ta bayyana matsayarta a duniya a fili game da wannan yaki.

“Kasashe da dama sun fito sun bayyana matsayinsu kan Isra’ila na amfani da ƙarfin da ya wuce ƙima kan Falasɗinu, kan mata da yara da tsofaffi da wuraren ibada wanda bai kamata ba.

“Idan wani zai ɓata rai yana yin zalunci ai ina ganin don ba zai ji ɗaɗi ba a yi shiru, in ji Kawu Sumaila.

Kudurin dai ya samu goyon bayan ‘yan majalisa kusan 45, waɗanda suka sama hannu gabainin a gabatar da shi gaban Majalisa.

A cewar Kawu Sumaila Majalisar ta yi na’am da wannan kudri.

Haka ma wasu shugabanin manyan addinai guda biyu na Najeriya, sun goyi bayan wannan kira.

Wannan shine karon farko da Majalisar Dattawan Najeriya ta yi kira da a kawo karshen yakin Isra’ila da Hamas da ya yi sanadiyar mutiwar dubban mutane.

Shi ma daya cikin sanatocin da suka goyi bayan kudurin, Sanata Iqra Aliyu Bilbis ya ce ganin yadda yakin ya rika kashe yara kanan da mata da tsofafi ya sa dole ne wani mai tausayi yayi kira da a hanzarta kai kayan agaji ga mabukata.

Bilbis ya ce Allah ne ya halice mu baki daya kuma ya ba kowa ‘yanci. Bilbis yayi kira ga Najeriya da ta hada hannu da sauran kasashe wajen kawo karshen rikicin tare da neman a kai kayan agajin cikin gaggawa domin a kawo wa mabukata sauki.

A bangaren manyan addinan biyu da ake da su a Najeriya, Musulunci da Kiristanci, Jami’i a Majalisar Koli ta Shari’a Aminu Inuwa Mohammed ya yi tsokaci cewa wannan abu da ke faruwa a zirin Gaza abu ne da ake yi tun shekaru sama da arba’in amma wanda ake yi a kwanannan shi ne ya fi zafi, domin ana ta kashe mutane da basu san hawa ba ba su san sauka ba musamman ma yara kanan da mata kamar yadda ya sanar da Muryar Amurka.

Saboda haka su na fata cewa Najeriya za ta dauki kwakwarar mataki wajen bada gudunmawa mai tsoka domin a ba mabukata agaji musamman ma a zirin Gaza inda kashe kashen ya fi yawa.

Aminu ya ce akwai tsari na Majalisar Dinkin Duniya da ya ba kowa dama na zama inda yake so, Majalisar Shari’a tana so a koma wannan tsarin domin kuwa ya tsuguna inda Allah ya ajiye shi.

Shi ma sakataren kungiyar CAN ta Arewa ta tsakiya Pastor Simon A. S. Dolly ya ce yana goyon bayan matakin da Majalisar Dattawa ta dauka dari bisa dari kan abinda Majalisar Dattawa suka yi. Dolly ya ce kashe kashe da ake yi a Gaza bai dace ba domin yara da mata ne ake ta kashewa wadanda ba su ji ba basu gani ba.

Dolly ya ce ba suna goyon bayan matakin harin da Hamas suka kai wa Israila ba ne, amma wannan kashe kashe ya yi yawa sosai. Saboda haka yana kira ga manyan addinan kasar da su ci gaba da yin addu’a na kawo karshen wanan yaki. Dolly ya ce Majalisar Dinkin Duniya ta yi dukanin mai yiwuwa wajen kawo karshen wannan yaki.

Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya kan yakin da ya barke a watan Oktoba inda kungiyar Hamas ta kai hari kan Isra’ila na nuni da cewa an lalata wuraren ibada 18, da wuraren zama 22,600 da cibiyoyin kiwon lafiya 19, da cibiyoyin ilimi 90, masana’antu 70 da ofisoshin watsa labarai 49.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here