Home Ilimi Ranar Malamai ta Duniya: ‘Yadda Darajar malanta take kara zubewa a Najeriya’

Ranar Malamai ta Duniya: ‘Yadda Darajar malanta take kara zubewa a Najeriya’

184
0
Dalibai akan dutse

Yayin da ake bikin ranar malamai ta duniya a ranar 5 ga watan Oktobar kowacce shekara, masu sharhi sun ce malamin da ke koyarwa a Najeriya bai cancanci ya yi wannan bikin ba.

Taken ranar malaman ta bana shi ne “Malaman da muke buƙata domin ilimin da muke so”, dole ne duniya ta tashi tsaye domin magance ƙarancin malamai.

Bikin na bana so yake duniya ta mayar da hankali kan yadda za a magance matsalar raguwar malamai, a kuma samar da hanyoyin da za a riƙa yawansu a ko da yaushe.

Hukumar raya ilmi da kimiya da al’adu ta Majalisar Ddinkin Duniya UNESCO tace samar da yanayi kyakkyawa da kuma tsarin karatu mai ɗorewa shi ake so ya zama burin al’ummar duniya.

A Najeriya ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ake fuskanta a bangaren koyarwa shi ne ƙarancin malamai, musamman kuma a makarantun firaimare da ake kallo a matsayin tushe ko kuma ginshikin ginin ilimin ɗan adam.

BBC ta zanta da wasu malamai a Najeriya kuma wani daga cikinsu ya ce akan samun makarantar firaimare da ke da malamai biyu kacal, shugaban makarantar da kuma malami guda ɗaya tal.

“Ta yaya waɗan nan mutane biyu za su iya aikin raino? an dakatar da malamai da dama a baya kuma har yanzu ba a ce ga halin da ake ciki ba kan lamuransu. Magana ta gaskiya lamarin koyarwa a arewacin Najeriya kullum ƙara durƙushewa yake yi,” in ji malamin.

Baya ga wannan a makarantun da ake da malamai kuma za ka tarar suma suna da nasu matsalolin na daban, kamar ƙarancin albashi, in ji wata malama.

“Albashi dai ba isa yake yi ba, malamin makaranta yana matuƙar shan wuya. Kuɗin da ake biya ko shi kaɗai ne ba za su iya riƙe shi zuwa wani watan ba”.

Kullum masu sharhi na ɗora laifin taɓarɓarewar ilimin kan hukumomi. Sai dai kuma su suna cewa suna iya ƙoƙarinsu domin inganta ilimin.

Sai an tashi tsaye kan a dawo da ƙimar malamin makaranta

Ta yaya za a inganta tsarin koyo da koyarwa domin dawowa da malamai irin ƙimar da suke da ita a a Najeriyar jiya?

Wannan ce tambayar da BBC ta yi wa Farfesa Musa Garba Maitafsir, shugaban cibiyar horas da malaman makaranta ta Najeriya ta NTI da ke Kaduna.

Ya fara da bayanin wannan rana da muhimmancin da take da shi a idanun ƙasashen da suka san ƙimar malamai, amma ba irin su Najeriya ba.

A ganinsa ma bai kamata a ce malamin makaranta a Najeriya zai shiga sawun jerin masu murna da ranar malamai ta duniya ba, saboda duk yanayin da ake tsammani a samar domin jin dadin koyo da koyarwa malamin Najeriya bai san shi ba.

“A Najeriya daga mai zaman banza sai malamai, abin da nake nufi shi ne, za ka ji ana cewa gwara a samar masa ko da koyarwa ce maimakon zaman banza da yake a unguwa,” in ji Farfesa Musa Maitafsir.

Ya ce a yanzu malamai ba shi da daraja a Najeriya, a baya da malami yake da ƙima ko yarinya yake neman aure babu mai tunkararta, saboda ko waye yasan malamin nan zai kayar da shi.

“Yau duk yarinyar da aka bai wa malami aurenta cikin biyu ne, ko bata da wani galihu, ko kuma ta rasa kwastam ko mai sayar da mai ko makamantansu”.

A cewar Farfesan abin da ya kawo taɓarɓarewar wannan lamari, akwai matsalar albashi. A yau akwai malamain firaimare da yake ɗaukar ƙasa da dubu 20 albashinsa.

“Kana ɗaukar albashin dubu 20 a matsayin malamin makaranta ko a idon matarka ba za ka yi daraja ba, domin kuwa waɗannan kudade ko naman kwana 30 ba za su ishe ka saya ba ga iyalanka,” Farfesan ya fada cikin jimami.

Da albashin malami zai fi na masu aiki a ofis, da sai ka ga ma’aikata na ajiye aikinsu suna komawa koyarwa.

Idan ka bayar da albashi mai kyau zai bai wa gwamnati damar tantance malamai masu inganci da suka cancanta.

Za ka tarar a takardar biyan albashi akwai malamai kusan 30 a firaimari guda, amma idan kaje bayan hedimasta babu wanda za ka gani sai malami daya ko biyu, halain da ake ciki a yau kenan a Najeriya. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here