Home Addini Ranar Karfafawa Mata Sa Hijabi

Ranar Karfafawa Mata Sa Hijabi

210
0

Ganin yadda hijab yake da tasiri  wajen suturta jiki tare da kare martabar mai sanye da shi, ya sanya kungiyoyin mata masu da’awa ke karfafa mata musulmai anfani da shi.

A gefe guda kuma, saboda illar da ciwon kansa ke da shi kan mutane ya sa hukumar lafiya ta duniya ta ware rana musamman don wayar da kan alumma akan wannan cutar.

Shi yasa hadakar kungiyoyin ‘yan uwa mata a Musulunci suka gudanar da taron ranar karfafawa mata sa hijabi Wato World Hijab Day da kuma ranar wayar da kai game da cutar daji wato world Cancer Day, a rana guda.

Taken ranakun na wannan shekarar shine hijabi yafi gaban lullubi kuma kowa ya cancanci samun maganin cutar daji.

Shugabar kungiyar mata masu da’awa ta Najeriya kuma daya daga cikin wadanda suka shirya taron Hajiya Rahma Musa Sani, ta ce duk da cewa suna samun nasara game da yadda ake musgunawa mata masu saka hijabi a wasu guraben aiki amma baza su karaya ba har sai hakar su ta cimma ruwa.

Hajiya Aisha Yabawa Bukar Ali wacce ta wakilci Hajiya Amina Namadi Sambo ta ja hankalin mata game da saka hijabi a kowani yanayi.

A nasa bangaren shugaban majalisar malamai a Abuja sheikh Ibrahim Muhammad Duguri ja hankalin mata tare da bayyana cewa a shari’ance babu wata rana da aka ware ta hijabi domin duk mace musulma ya kamata ace tana cikin hijabi a duk lokacin da zata fita.

Dr. Shehu Umar kwararren likita ne a fannin ciwon daji ya yi bayani cewa sanya hijabi na bada kariya daga hasken rana da ka iya haifar da dajin fata wato “skin cancer”.

Kawararriyar likita a fannin, Dakta Basira Hannafi Lawal ta ce irin wadannan taron kan taimaka wajen fahimtar da jama’a game da muhimmancin zuwa asibiti.

A duk shekara ana samun mutum miliyan ashirin dake kamuwa da cutar daji a fadin duniya, yayin da ake samun mutum dubu dari da ashirin da biyar dake kamuwa da cutar a Najeriya. (Muryar Amurka).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here