Home Siyasa PDP ta gargaɗi mambobin ta na majalisa cewa tilas su riƙa yi...

PDP ta gargaɗi mambobin ta na majalisa cewa tilas su riƙa yi wa jam’iyya biyayya

160
0

Shugaban Riƙo na Jam’iyyar PDP, Umar Damagum, ya ja kunnen ‘yan majalisar tarayya, zaɓaɓɓu na PDP su 116 cewa tilas ne su yi wa jam’iyyar PDP wadda ta kai su wannan matsayi biyayya.

Damagum ya bayyana hakan a ranar Talata a lokacin da ya ke ganawa da su a Abuja, taron da aka yi ganin lokacin zaɓen shugabannin majalisun biyu na ƙara gabatowa.

Taron ya zo ne daidai lokacin da kamfen ɗin neman Kakakin Majalisa da Mataimakin Kakakin Majalisa na ƙara zafi.

PDP na da wakilai 116, waɗanda zaɓen Kakakin Majalisa ya raba kawunan su.

Da yawan su dai sun afka cikin ƙungiyar ‘yan maja, guruf ɗin da ya amince zai bi tsarin APC na zaɓen shugabannin majalisa bisa tsarin karɓa-karɓa.

Kingsley Chinda ɗan PDP daga Ribas ne shugaban maja, shi da Bello Kumo daga Jihar Gombe.

Damagum ya ce tabbas ya na sane cewa PDP na cikin rigingimu, to amma fa kuma ita da kan ta za ta iya magance matsalolin ta a cikin gida.

“Sai kun jajirce. Kuma ku yi wa ƙasar ku biyayya. Daga nan sai jam’iyyar ku. Biyayya ga ƙasa shi ne farko, domin sai da ƙasar ce za ka iya zama ɗan majalisa.”

PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa wakilan APC, PDP, LP, NNPP da wasu sun ƙulla ‘maja’.

Gamayya ko ‘majar’ ‘Yan Majalisar Wakilai na Ƙasa waɗanda za su yi wakilci daga 2023 zuwa 2027, daga jam’iyyu takwas, sun amince su kiyaye da bin tsarin karɓa-karɓa da APC ta shigo da shi a shugabancin majalisar.

Sun amince da sharuɗɗan karɓa-karɓa ɗin a ranar Talata, yayin da su ke ƙaddamar da gangamin ‘maja’ ɗin da su ka yi, wadda su ka raɗa wa sunan Turanci, “Join Task”, a Abuja.

An haɗa mambobin maja ɗin daga jam’iyyu takwas da su ka haɗa da APC, PDP, LP, NNPP, APGA, SDP, ADC, da YPP.

Sai dai kuma ba dukkan mambobin majalisar kakaf ba ne su ka amince da shiga wannan majar.

Da ya ke magana lokacin ƙaddamar da maja ɗin su, Honarabul Bello Kumo, ɗan APC daga Gombe, ya ce har yanzu mambobin maja ɗin ba su da ɗan takarar da su ke goyon baya. Amma su na jiran su ga tsarin karɓa-karɓar da APC, jam’iyya mai mulki kuma mafi rinjaye a majalisa za ta fitar.

“Mu saƙon mu ga ga ‘yan Najeriya a daidai wannan lokaci shi ne, a shirye mu ke domin mu yi aikin bunƙasa ƙasa da inganta rayuwar mu.

“Idan kuwa mu na son cimma wannan kyakkyawan ƙudiri na mu, to kenan tilas sai mun yi aiki kafaɗa-da-kafaɗa da ɓangaren Zartaswa na Gwamnati, amma kuma ba tare da sun yi watsi da ‘yancin mu na masu doka ba kuma masu ‘yancin su.

“Mu dai abin da ya fi damun mu shi ne haɗin kan ƙasar nan da kuma zaman lafiya da kwanciyar hankali sai kuma nagartar Majalisa ta 10. ”

Shi ma Aliyu Madaki, ɗan NNPP da Kano, ya ce mambobin majalisa ba za su zama gugar-yasa ga ko ma wane ne zai zama Kakakin Majalisa ba. Amma dai kawai su na bai wa APC dama ce su fitar da shugabanni bisa tsarin da duniya ta fi gamsuwa da shi.

Ya ce dama ko’ina a dimokraɗiyya, ana bai wa jam’iyyar da ta fi rinjaye damar fitar da shugabannin majalisa.

“Ni da na fito daga jam’iyyar adawa, za mu yi adawa sosai, amma ba bisa son kai ba. Zan yi adawa ne domin mu wanzar da abin da zai kawo wa ƙasar nan ci gaba mai mai albarka.”

APC na da wakilai 177, PDP 116, LP 38, NNPP 19. APGA na da 5, ADC 2, SDP 2, sai kuma YPP 1.

Yayin da Kumo na Gombe ne shugaban maja, Kingsley Chinda na PDP daga Ribas ne shugaba na biyu. Sai Ali Madaki na NNPP daga Kano ke Sakataren maja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here