Home Kwadago NURTW: Ku Bawa Kwamitin Riko Damar Shirya Zabe Mai Inganci – Inji...

NURTW: Ku Bawa Kwamitin Riko Damar Shirya Zabe Mai Inganci – Inji Yasin

175
0
NURTW 2

An yi kira ga Yan Kungiyar Motocin Sufurin Haya na Kasa wadanda ake kira da NURTW da su bawa Shugabancin Riko na Kungiyar Hadin Kai domin tabbatar da sahihin zabe da zai haifar da Shugabanci na Kasa da kowa zai yi alfahari da shi.

Shugaban Kwamitin Amintattu kuma shugaban Sasantawa na Kungiyar, Alhaji Najeem Usman Yasin ne ya yi wannan kira jim kadan da kammala wani taro na masu ruwa da tsaki domin kawo karshen rigingimu da su ka dabaibaye kungiyar da aka gudanar a ofishin Kungiyar na Kasa da ke Garki a Abuja a ranar Talata.

Ya ce makasudin taron shine domin a kubutar da Kungiyar da ga barazanar rikici na shugabanci da ya fuskanto Kungiyar sakamakon son zuciya na wasu da ga cikin Shugabannin Kungiyar wadanda wa’adinsu ya kare.

Alhaji Najeem ya ce sakamakon wani taro da Yankunan Arewa guda uku suka yi wanda ya bayar da shawarwari kuma aka samu amincewar wa su Yankuna na Jihohin Kudu, na Kwamitin sa da ya gudanar da zabe a dukkanin shiyyoyi guda 6 da su ke kasarnan domin samar da shugabanni da za su shugabanci Kungiyar a sabon zango.

Ya ce Kundin Tsarin Mulki na Kungiyar sashi na 31 ya bawa Kwamitinsa dama na da ya kira taro na sasantawa domin kawo karshen duk wata matsala da ta addabi Kungiyar.

Najeem ya kara da cewa, Kwamitinsa ya sami nasarar hada taro na Kasa wanda ya sami halartar Shugabanni da Sakatarori da Ma’aji-ma’aji da ga Jihohi 25 da ke kasarnan. Har ila yau, taron ya sami halartar tsofaffin Shugabanni da sakatarorinsu da Ma’aji- ma’aji da wadannan Jihohi.

Taron ya sami amincewar da a gudanar da zabe a shiyyoyi 6 na Kasarnan wanda zai samar da wakilci na mutum uku-uku da ga kowanne shiyya domin samar da Shugabanni na Kasa.

Za’a gudanar da zaben na shiyya – shiyya a ranar 5 ga watan Octoba sannan za’a rantsar da wadanda aka zaba ranar 25 ga watan na Octoba a Abuja gabanin zaben Shugabannin Jihohi da za’a gudanar a karshen watan na Octoba na wannan Shekara.

A sakamakon haka, Alhaji Najeem ya yi kira ga Yan Kungiyar masu sha’awar takara da su koma shiyyoyin su domin su nemi jama’a da su zabe su a mukamai da aka warewa kowacce shiyya ba tare da wata matsala ba.

Najeem ya yi alkawarin ganin cewa ya gudanar da zabe na gaskiya ba tare da la’akari da wani banbanci ba domin samar da shugabanci na gari da zai kawo cigaba mai dorewa a Kungiyar.

Ya ce irin wannan zabe na gaskiya da adalci da ya gudanar a shekara ta 2019 shine ya sa mutane suke ganin kimarsa kuma su ke kwadayin ganin an sake gudanar da makamancin irinsa a 2023 domin samar da shugabanci na gari.

A karshen taron an yabawa Hukumomin Jami’an tsaro da suka hada da Shugaban Yansanda Na Kasa (IGP) da Shugaban Jami’ana Tsaro na Farin Kaya (DSS) da Hukumar NCDCS da Kwamishinan Yansanda na FCT a bisa gudunmawar da suka bayar na samar da tsaro domin ganin an gudanar da taron ba tare da wata hatsaniya ba.

Kwamitin a Karshe ya yabawa, Alhaji Najeem Usman Yasin a bisa irin gudunmawar da ya bayar wajen ganin ya hada kan Yan Kungiyar sun zama tsintsiya madaurinki daya. Tare da fatan cewa zai cigaba da bayar da irin wannan gudunmawa anan gaba domin cigaban Kungiyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here