Home Zirga zirga NRC ta sanar da dawo da zirga-zirgar jiragen kasa tsakanin Abuja da...

NRC ta sanar da dawo da zirga-zirgar jiragen kasa tsakanin Abuja da Kaduna

176
0

Hukumar da ke kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya, NRC ta sanar da masu mu’amulla da ita cewa tana farin cikin dawo da zirga-zirgar jiragen kasa tsakanin biranen Abuja zuwa Kaduna.

Hukumar ta dakatar da dukkan jigilar fasinjoji kan wannan hanyar ne a ranar Juma’a 27 ga watan nan na Janairu 2023 a sanadiyyar gocewan da wani jirgin kasa yayi a kusa da tashar Kubwa cikin wannan yinin.

Cikin wata sanarwa da daraktan gudanarwa na NRC Niyi Alli ya sanya wa hannu, hukumar za ta koma daukan fasinjoji daga Talata 31 ga watan Janairun 2023.

Ta kuma sanar da jadawalin jiragen da za su rika zirga-zirga kamar haka: AK1 zai tashi daga Idu da karfe 7:00 na safe KA2 zai tashi daga Rigasa da karfe 10:15 na safe AK3 zai tashi daga Idu da karfe 1:20 na rana KA4 zai tashi daga Rigasa da karfe 4:30 na yamma.

Sai dai a ranakun Laraba, jirgi mai lamba AK1 ne kawai zai tashi daga Idu zuwa Rigasa da karfe 7:00; inda jirgi mai lamba KA4 zai tashi daga Rigasa zuwa Idu da karfe 4:30 na yammacin wannan ranar. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here