Home Siyasa “Ni Da Gwamna Uba Sani Tsintsiya Guda Mu Ke…”, Inji Speaker...

“Ni Da Gwamna Uba Sani Tsintsiya Guda Mu Ke…”, Inji Speaker Tajuddeen Abbas

146
0
Abbas Uba Sani

Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani da Kakakin Majalisar Wakilai Tajuddeen Abba sun karyata jita jitar da a ke cewa ba sa ga maciji a tsakanin su duk da cewa sun fito da ga Jiha guda.
Sun karyata wannan jita jita ne lokacin da Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani ya kai wa Kakakin Majalisar Wakilai Tajuddeen Abba ziyara a ofishin sa da ke Majalisar Wakilai da ke Abuja a ranar Laraba.
Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas wanda ya yiwa Yan Jaridu Karin haske game da ziyarar in da ya karyata jita-jita da ke zagayawa cewa da Gwamna Uba Sani da Shi ba sa jituwa. “ ina amfani da wannan dama domin in karyata jita-jita da ke zagayawa cewa duk in da aka sami Spika a Jiha da Gwamna ba sa ga Maciji. Mu a Jihar Kaduna kammu a hade ya k e kamar yadda ku ka ji da ga bakin Gwamna Uba Sani cewa sun kawo mun wannan ziyara ne domin nuna goyon bayan su a gare ni”.
Spika Abbsa ya kara da cewa su a Jihar Kaduna kan su a hade ya ke su da Minista da dukkan Yan Majalisun su da ke Jihar Kaduna kuma a shirye su ke su yi aiki tare domin kawo cigaba a jihar su da ma kasa baki daya.
Tajuddeen Abba ya godewa tawagar da ta kawo masa ziyara inda ya yi mu su fatan alheri na ganin sun sami nasara akan abubuwan da suka saka a gaba na kawo cigaba a Jihar Kaduna da ma Kasa baki daya.

Uba Sani at NASS
Tun da farko Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani ya ce makasudin ziyarar ta su shine domin su nu na goyon bayan su ga Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas na irin shugabanci da ya ke bayarwa a Majalisar tare da yi ma sa fatan alheri.
Gwamna Uba Sani ya kara da cewa su na alfahari da Tajuddeen Abbas ganin yadda ya jajirce wajen ganin ya bayar da shugabanci mai inganci domin samun nasarar Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu wajen ganin Najeriya ta samu cigaban da ake bukata.
Ya ce Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya na mai alfahari da irin Shugabancin Tajuddeen Abbas. “ Na tattauna da Shugaban Kasa kuma sau uka ya na cewa ya na da alfari da Shugabancin Abbas sa bo da irin jajircewa da ya ke yi wajen ganin an sami kyakkawan fahimta tsakanin Fadar Shugaban Kasa da Majalisar Wakilai”
Uba Sani ya kara da cewa makasudin ziyarar su, su da Ministan su Balarabe Abbas Lawan da sauran Yan Majalisun su shi ne domin su nu na goyon bayan su ga Tajuddeen Abbas tare da ba shi kwarin gwiwar cewa su na tare da shi dari bisa dari kuma a shirye su ke su ba shi duk irin gudunmawar da ya ke bukata domin samun nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here