Home Cinikaiyar Zamani NASSI Ta Yabawa Majalisar Wakilai Na Samar Da Doka Da Zata Inganta...

NASSI Ta Yabawa Majalisar Wakilai Na Samar Da Doka Da Zata Inganta Kayayyaki Da A Ke Sarrafawa A Najeriya

56
0
IMG 20240419 WA0000

Shugaban Kungiyar Masu kananan Masana’antu ta Najeriya (Nassi), Chief Dr. Solomon Vongfa ya yabawa yunkurin Maja)lisar Wakilai na yin Doka don inganta kayayyaki da ake samarwa a cikin gida.

Ya yi wannan yabo ne jimkadan da kammala zama da Majalisar ta shirya na ma su ruwa da tsaki akan kayan da ake samarwa anan Najeriya don jin ra’ayin su.
Chief Vongfa ya ce idan wanna Doka ta tabbata zai taimaka wajen habaka  kasuwanci a Najeriya ta fannoni da dama.
Ya ca samar da Dokar zata kare yancin yan kasuwa ta fannin fifita kayan da ake samarwa anan cikin gida fiye da wadanda ake shigo da su daga kasashen waje.
  1. CamScanner 04 18 2024 15.12 1
Bayan haka, ya ce dokar zata bawa Yan kasuwa dama ta yadda za su rinka inganta kayayyaki da ake samarwa a cikin gida Najeriya.  Domin hakan zai bawa Yan kasuwar dama su yi gogayya da kayayyaki da ake shgowa da su.
Shugaba Vongfa ya kara da cewa samar da wannan Doka na nufin samar da kudaden shiga ga kananan Masana’antu wanda hakan zai haifa da aiyukan yi da yalwatar arziki ga Yan Najeriya.
Sabo da haka, idan Dokar ta tanbata za su yi duk mai yiwu wa wajen kare kananan Masana’antu ko da a gaban kotu ne domin Dokar ta ba su dama na kare kasuwancin su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here