Home Addini NASS: Yadda Yan Majalisar Taraiya Ta 9 Suka Samar da Sama Da...

NASS: Yadda Yan Majalisar Taraiya Ta 9 Suka Samar da Sama Da Naira Miliyan 500 Don Gina Masallaci

157
0

Yan Majalisar Taraiya sun kashe sama da Naira Miliyan Dari Biyar domin samar da Masalacin Juma’a na alfarma a harabar Majalisar domin su rinka gudanar da Sallar Juma’a da sauran salloli biyar a Majalisar ta Kasa.

Shugaban Kwamitin gudanar da aikin masallacin Sanata Malam Ibrahin Shekarau ne ya sanar da haka a wajen kaddamar da Masallacin a jiya Juma’a.

Sanata Shekarau ya ce, Musulmin Yan Majalisar Taraiyar ne tare da sauran ma’aikatan Majalisar su ka tara wadannan makuden kudede domin ganin an samar da wannan masallaci don gudanar da ibadar Allah.

Ya ce daga cikin sama da Naira Miliyan dari biyar (N500m) da saba’in da aka tara, an kashe sama da naira miliyan dari hudu (N400m) domin samar da masallacin mai alfarma. Kuma an sami rarar kudi sama da Naira Miliyan dari  (N100m) wacce za’a cigaba da anfani da ita wajen kula da masallacin.

Yayin kaddamar da Masallacin, Mataimakin Shugaban kasa, kuma tshohon Sanata a Majalisar ta Tara, Sanata Kashim Shettima wanda ya Wakilci Shugaban Kasa, Ahmad Bola Tinubu  ya yabawa yan kwamitin gina masallacin na tabbatar da shi a yanayi na kasaita wanda ya yi daidai da kowanne masallaci a duniya.

Kashim Shettima ya yabawa Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmada Lawan wanda shine ya amince da a rinka cire wadannan kudade da ga cikin albashin Yan Majalisar Taraiyar ta Tara domin samar da wannan Masallacin.

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya ce an dauki tsawon watanni tara ana cire wadannan kudade da ga asusun Yan Majalisar ta Tara su sama da mutum dari biyu da sittin (260).

Sanata Ahmad Lawan ya yabawa Yan Majalisar Taraiyar da su ka bashi hadin kai da goyon baya wajen ganin hakan ta faru.

Ya ce  wannan sadaukarwa da su ka yi tare da fatan Allah ya karbi wannan aiki da suka gudanar na ibada wanda sadakatu Jariya ne. Ya kara da cewa wannan aiki da sukayi za su girbi abun da suka shuka ko bayan rasuwar su ne.

A nasa Jawabin Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila wanda ya yi jawabin godiya ya ce, a aikin Allah ba’a bukatar godiya domin idan an aiwatar da aiki don Allah, Allan ne zai biya bawan na sa da mafificin sakamako.

Ya bukaci Yan Majalisar da su saka kasarnan wajen addu’a a ko wanne lokaci suke gudanar da ibada a wannan Masalci da fatan Allah zai tallafawa Shugabanni domin gudanar da aiyuka a kasarnan da za su kawo sauki na matsi da ake fama da shi a kasarnan.

A nasa jawabin, Sanata Barau Jibrin ya ja hankalin Yan Majalisar ta goma (10) da su dora da ga inda aka tsaya ta hanyar cigaba da kula da wannan Masallaci ta hanyar bayar da gudunmawa ta kudi akai akai domin tabbatar da tsafta da kula da masu yiwa Masallacin hidima.

Ya ce, a kasar Saudia, Masallacin Harami da Masallacin Madina su na samun kulawa ta musamman sabo da ana biyan wadanda suke yiwa Masallatan hidima.

Sanata Barau ya kara da cewa kula da masallacin ya rataya ne akan dukkan Yan Majalisu masu zuwa anan gaba. Wanda ya ce idan sunyi hakan don Allah su ma za su shiga cikin ladan da Allah Subuhanahu wa Ta’ala zai rinka bawa duk wanda ya gina sadakatu Jariya.

Taron kaddamar da Masallacin ya sami halartar manyan mutane da ga cikin su akwai Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero wanda ya wakilci Sarkin Musulmi, Abubakar Sa’adu III. Wan da ya ja hankalin Yan Majalisar da su saka tsoron Allah wajen gudanar da aiyukan su.

Ya ce, idan suka yi hakan, Allah zai shiga cikin lamarin su wanda zai haifar da cigaba gagarumi a kasarnan. Shi kuma talaka zai samu sauki wajen rayuwar sa.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Sarki Bauchi, da Yan Majalisar Taraiyar masu yawa da tsofaffin  Maga Takardan Majalisar da sauran manyan mutane daga sassa daban daban daga kasarnan.

An gudanar da sallar Juma’a ta farko a Masallacin da misalin karfe biyu na rana, sai dai za a cigaba da gudanar da Sallar Juma’a a Masallacin da misalign karfe daya na rana da sauran salloli na kasussalawati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here