Home Siyasa Nasarar Kotun Koli: Yan Adawa, Adawa Ta Kare – Ko Zo Mu...

Nasarar Kotun Koli: Yan Adawa, Adawa Ta Kare – Ko Zo Mu Gina Jihar Kebbi

158
0
Kebbi Dept. Gov, Sen. Argungun

Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sen. Umar Abubakar Argungun da Shugaban Kwamitin Noma na Majalisar Wakilai, Hon. Bello Ka’oje sun yi kira ga yan adawa da ke Jihar da su jingine adawa su marawa Gwamnan Jihar Kebbi Dr. Nasiru Idris baya wajen tabbatar da aiyukan alheri da ya fara da za su kawo cigaba ga jihar baki daya.

Sun yi wannan kira ne jimkada bayan da Kotun Koli a Abuja ta aiyana Gwamnan ranar Juma’a a matsayin wanda ya sami nasara a zabe da aka gudanaar a shekara ta 2023; bayan da jam’iyar PDP ta kalubalanci nasarar ta sa a kotuna daban-daban.

Sanata Argungun ya ja hankalin Yan adawa akan cewa tunda Allah ya tabbatar da nasara ga Gwamnan ya kamata su rungumi kaddara su ba shi goyon baya a matsayin su na Yan Jihar Kebbi domin ya cigaba da aiyuka na alheri da ya fara domin gina Jihar.

Ya ce aiyuka da a ka fara wata manuniya ce akan irin kyawawan kudure-kudure da Gwannan ya ke da su na kawo cigaba a jihar musamman a bangaren Noma; in da ya ce kayayyaki na aikin Noma da aka raba wani soma tabi ne kawai ga al’umar Jihar Kebbi.

Sanata Argungun ya godewa, Yan Jam’iyar APC game da irin goyon bayan da suka bayar da jajircewa wajen ganin Jam’iyar ta sami nasara tare da yi musu alkawarin cewa ba za su basu kunya ba wajen kawo cigaba da zaman lafiya a jihar.

A na sa bangaren Dan Majalisar Wakilai da ke Wakiltar Bagudu da Suru a Majalisar Taraiya Hon. Bello Ka’oje shi ma ya bukaci Yan adawa da su marawa Gwamna goyon bayan su domin ya cigaba da aiyuka da ya fara na alheri. In da ya ce su ma Yan Jihar Kebbi ne sabo da haka su na da rawar da za su taka wajen gina Jihar.

Hon. Ka'oje 3

Hon. Ka’oje wanda ya ce kayayyaki noma da aka raba a Jihar a wannan satin ga manoma sama da mutum Dubu 20 manuniya ce na irin kyawawan kudure – kudure na inganta aikin Noma a matsayin su na manoma.

Dan Majalisar ya ce Gwamnan ya kaddamar da wani tsari na Noma da a ka yiwa lakabi da KADAGE wato yan Jihar su kara dagewa wajen aikin noma wanda burin gwamnatin shine domin su mayar da Jihar ta kasance ita ce kangaba wajen harkar Noma musamman na Shinkafa a kasarnan.

Ka’oje ya ce a matsayin sa na Shugaban Kwamitin Noma na Majalisar Wakilai sun hada gwiwa da Gwamnan Jihar wajen samar da tsare-tsare na Noma da zai tallafa wajen mayar da Jihar jagora akan harkar Noma a kasarnan.

Ya ce akwai yarjejeniya tsakanin Gwamnatin Taraiya karkashin Jagorancin Bola Ahmad Tinubu ta hanyar Ministan Noma da Gwamnatin Jihar Kebbi na samar kayayyakin Noma da bayar da horo tare da samar da iri masu inganci da za su samar da abinci da magance rashin aikin yi a Jihar.

Game da batun tsaro, ya ce Gwamnatin Jihar ta dauki matakai tare da hadin gwiwa da Gwamnatin Taraiya tare da Yan sakai wajen magance matsalar tsaro in da ya ce a halin yanzu an magance mtsalar tsaro da kashi 99.5; wanda hakan ya sa ba wani guri da ba’a nomawa a Jihar ko da rani ko da damina.

APC Chairman Yawuri Kebbi

Yusuf Alhassan, Shugaban Jam’iyar APC na karamar Hukumar Yawuri shi ma ya nuna farin cikin sa game da nasarar da aka samu a kotun Koli wanda ya ce wata dama ce da za ta kawo cigaba akan aiyuka na alheri da aka fara a Jihar.

In da ya yi kira ga Yan adawa da su rungumi kaddara su bawa Gwamnan goyon baya wajen ganin ya cigaba da aiyukan alheri da ya fara wanda ya ce burin Jam’iyar APC shi ne ta kawo cigaba da bunkasa tattalin arziki da samar da zaman lafiya mai dorewa a Jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here