Home Uncategorized NASARAR EKITI: YADDA AKASHA BIKI A VILLA

NASARAR EKITI: YADDA AKASHA BIKI A VILLA

159
0
PMB 3
PMB 3

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Yan Majalisarsa da Shugabannin Jam’iyar Apc da sauran ma’aikata musamman masu rike da mukaman Siyasa sun kasa boye farincikinsu a yayin da suke karbar sabon zabbaben Gwamnan Jahar Eikiti, Biodun Abayomi Oyebanji a Fadar sa.

Shugaban Jam’iyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu ne ya jagoranci tawagar Zabbben gwamnan zuwa Fadar Shugaban Kasa tare da rakiyar Gwabnan Jahar Jigawa, wanda shine shugaban zaben na Ekiti da kuma Gwamnan Jahar Kebbi, Atiku Bagudu.

Dukkanninsu sun kasa boye farincikinsu a yayin da sukakai wannan ziyara. Shikansa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari cike yake da farin ciki maras misaltuwa.

A wata sanarwa, wadda Mai bashi Shawara akan Harkar Yada Labarai, Femi Adeshina ya fitar Buhari yace:

“ Naji dadi matuka yadda Gwamnonin APC suka hade kansu suka marawa dantakararmu, Oyebanji baya. Ina da kyakkyawan yakini cewa Jam’iyar APC tana samun nasara; wanda hakan ke nunawa abubuwa sunayin kyau. Ina taya Shugaban Jam’iyar APC murnar wannan nasara. Ina fatan za’a cigaba da wannan kokari”.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace ya hana idonsa barci domin ganin yadda zaben ya gudana ranar 18 ga Yuni. Ya kara da cewa abun dayafi burgeshi shine yadda aka gudanar da zaben cikin nutsuwa da yadda jami’an Tsaro suka gudanar da aikinsu a bisa tsari.

Shugaban Jam’iyar ta Kasa, Abdullahi Adamu yace nasarar da aka samu daga Allah take kuma suna fatan wannan nasara zata bisu Jahar Osun dama babban zabe da za’a gudanar a shekara mai zuwa.

Anasa Jawabin Shugaban Zaben Jahar Ekiti, Gwamnan Jahar Jigawa, Badara Abubakar yace nasarar da aka samu ta biyo bayan irin goyon baya da shugaban Kasa Muhammadau Buhari yake bayarwane wajen ganin Jam’iyar APC ta zama tsintsiya madaurinki guda.

Zababben Gwamnan, Oyebanji yace nasarar daya samu ta biyo bayan irin gudunmawar shugaban kasa Muhammadu Buhari ne daya bayar kuma yana da kwarin gwiwar cewa hakan idan ya cigaba da faruwa zai tabbatar da nasara a zaben Osun dama na kasa da za’a gudanar a badi in Allah yakaimu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here