Home Siyasa Najeriya Zata Cigaba Ne Kawai Idan An Daina Rayuwar Karya – Inji...

Najeriya Zata Cigaba Ne Kawai Idan An Daina Rayuwar Karya – Inji Hon. Azare

180
0
Hon. Azare

An baiyana cigaban Najeriya a cikin shekaru 63 da samun yancin kai na mai hakan rijiya sakamakon cinhanci da rashawa da rayuwar karya da aka gina kasar akai tun lokacin da aka samu yancin kai ya zuwa yanzu.

Dan Majalisar Taraiya mai Wakiltar Mazabr Katagum, Hon. Auwalu Abdu Gwalabe Azare, ne ya fadi haka a hirarsa da Yan jaridu a ofishinsa da ke Abuja ranar Juma’a.

Hon. Azare ya ce Najeriya ba zata cigaba ba har sai an daina rayuwar karya. Inda ya ce kasar da ake kashe kashi 70 na kasafin kudin kasar akan mutane kasa da kashi 10; ya yin da kaso 30 kuma ake kashe shi akan kaso 80 na al’umar kasar.

Dan Majlisar ya ce domin mutane su fahimci wannan bayani nasa ya da kyau su lura cewa wadanda suke rike da madafan iko akasarnan daga kananan hukumomi da Jihohi da Gwamnatin Taraiya dukkanin su basu kai mutum miliyan20 ba a cikin mutane sama da mutum miliyan 200 da ake ikirarin ana da su amma ana kashe mu su kaso 70 na kasafin kudin kasar.

Har ila yau, ya kara da bayanin cewa kaso 30 na kasafin kudin kasar da shi ake gina tituna da makarantu, da asibitoci da wutar lantarki da samar da ruwan sha da sauran aikace aikace na cigaba.

Hon. Azare ya ce idan ana so Najeriya ta cigaba to ya zamo dole mu gayawa kammu gaskiya, cewa rayuwar karya muka gina kammu akai sabo da haka sai mun yarda mun gyara idan muna so Najeriya ta ci gaba.

Dan Majalisar ya bayar da misali da irin kasashe da muka samu Yancin akusan lokaci daya kamar su India da ma wadanda suke bayan mu irin su  Dubai da Egypt da Indonesia da sauransu wadanda ya ce sunyi mana fintinkau wajen cigaban.

Hon. Azare ya ce Cinhanci da rashawa shine kashin bayan rashin cigaban kasarnan inda ya ce dole sai kowa ya yarda ya yake shi da gaskiya idan har ana so Najeriya ta cigaba.

Ya yin da ya bada misali da cire tallafin mai da aka yi, inda ya ce dalilin shine ana bayar da tallafin mai ne sabo da Yan Najeriya amma masu gidajen mai sai su fice da kaso 80 na mai da aka basu zuwa kasashen Africa inda suke sayar da shi akan kudi kimanin Naira 900 ya yin da ake sayar masu da mai a kasa da Naira 200.

Ya ce irin wadannan halaye na cinhanci da wadanda suke gudana a ofisoshi da gidaje toh! ya zama dole a ya ke su idan har ana so Najeriya ta ci gaba amma idan aka yi akasin haka to ba da gaske ake yi ba wajen ganin Najeriya ta cigaba.

Sai dai Hon. Azare ya ce duk da irin wadannan kalu bale da ake fuskanta Najeria ta samu cigaba ta fannin yawan al’umma da tituna da gine-gine da sauran su amma akwai bukatar su fi haka idan za a kwatanta da kasashe da suke sa’annin Najeriya  dama kannenta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here