Home Kotu da 'Yan sanda Najeriya ta kama sassan jakuna da ƙayoyin kifin Shark da aka yi...

Najeriya ta kama sassan jakuna da ƙayoyin kifin Shark da aka yi shirin fita da su waje

220
0
Jakuna shark

Hukumar kwastam a Najeriya ta kwace tarin mazakutar jakuna da kuma ƙayoyin kifi da kuɗinsu ya kai N1.23bn a filin jirgin saman Legas wanda aka yi niyyar fita da su zuwa China da Hong Kong.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Alhamis, ta ce ba ya ga al’aurar jakunan ta kuma samu nasarar kama wasu haramtattun kayayyakin.

Kwamandan hukumar a jihar, Muhammed Yusuf, ya bayyana cewa wani ɗan ƙasar China ne ya ɗauko al’aurar jakunan na maza daga garin Abakaliki na jihar Ebonyi da nufin tafiya da su ƙasarsa ta asali.

“Jakuna na cikin dabbobi da ke barazanar karewa, sai muka fara tunanin dalilin da ya sa suka fito daga wannan bangaren,” in ji sanarwar hukumar.

Ya ce idan ba a ɗauki matakin da ya kamata ba jakuna za su kare a faɗin ƙasa. Hukumar ta ce an kama ɗan Chinar kuma ana ci gaba da bincike.

Game da ƙayoyin kifin da aka kama kuwa, hukumar ta ce ana ci gaba da bincike domin gamo daga wajen da aka kawo su saboda ganin cewa ba bu isassun nau’in kifin shark a tekun Najeriya.

A ɗaya ɓangaren, hukumar ta ce daga watan Janairu zuwa Yulin 2023, ta samu kuɗaɗen shiga da suka kai N47.24bn. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here