Home Siyasa Najeriya ta fi samun ci gaban tattalin arziƙi lokacin Obasanjo – El...

Najeriya ta fi samun ci gaban tattalin arziƙi lokacin Obasanjo – El Rufa’i

190
0
elrufai

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El – Rufai ya ce wa’adi na biyu na tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo cike ya ke da yalwatuwar arziki, samar da ayyukanyi da kuma rage hauhawar farashin kaya a Najeriya.

El Rufa’i ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin wani taron Afrika da ya gudana a Afrika ta Kudu, wanda aka tattauna kan samar da tsari mai kyau da zai bunƙasa tattalin arziƙin ƙasashen nahiyar.

Tshon ministan ya ce “Muna da hukumar tsare-tsare sai dai ba ta aiki yadda ya kamata.”.

“Idan ka dubi tsari tattalin arzikin Najeriya lokacin da ya fi samun tagomashi shi ne shekaru huɗu zuwa biyar na wa’adi na biyu na tsohon shugaban Najeriya Obasanjo daga 2003 zuwa 2007, lokacin da a karon farko ƙasar ta koma tsarin da yake mai inganci da ya dace kuma muka yi sa’a,” in ji El Rufa’i.

Obasanjo ya jagoranci Najeriya daga shekarar 1999 zuwa 2007, kuma shi ne shugaban farar hula na farko bayan komawar ƙasar kan tsarrin dimokraɗiyya.

Shi kuwa El Rufa’i ya yi ministan babban birnin ƙasar Abuja. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here