Home Labaru masu ratsa Zuciya Mutumin da ya kwana 31 yana cin tsutsa a daji domin ya...

Mutumin da ya kwana 31 yana cin tsutsa a daji domin ya rayu

239
0

Wani mutum ɗan ƙasar Bolivia ya bayyana yadda ya riƙa rayuwa a dajin Amazon har na kwana 31 bayan ya ɓata.

Jhonattan Acosta, ɗan shekara 30, ya ɓace wa abokan tafiyarsa hudu lokacin da yake farauta a arewacin Bolivia.

Ya ce ya riƙa shan ruwan saman da ya riƙa tarawa a cikin takalminsa da tsutsa da sauran kwari domin ba zai iya fita ba, saboda ya laɓe wa damisa da sauran halittu masu farauta.

A ƙarshe dai wata tawagar masu bincike ce ta gano Mr Acosta da abokansa wata guda bayan ɓatan sa.

“Abin mamaki ne, ban taɓa jin cewa mutane za su yi ta neman mu na tsawon wannan lokacin ba,” ya faɗi haka ne lokacin da yake kuka.

“Na ci tsutsotsi, na ci ƙwari, ba za ku yarda da irin rayuwar da na yi ba a wannan kwanaki,” ya shaida wa wani gidan talabijin Unitel. Ya riƙa cin wasu ganyaye da babu mai ci sai dabbobi.

“Na yi wa Allah godiya, saboda ya ƙara ba ni rayuwa mai kyau.”

Iyalansa sun ce da buƙatar su sake zama tare domin jin yadda aka yi ya rayu a cikin wannan daji, amma za su tambaye shi ne a hankali saboda idan yana tunawa abin ba ya yi masa daɗi.

A cewar waɗanda suka gano shi, sun ce Mr Acosta ya ɓata ne ɗauke da kaya masu nauyi kilogiram 17 ya kuma ji ciwo a idon sawunsa sannan yana cikin matsananciyar buƙatar ruwan sha, amma duk da haka yana iya ɗingishi yana tafiya.

“Ɗan uwana ya shaida mana cewa lokacin da ya ji ciwo a idon sawunsa a kwana na huɗu ne da ɓatansa, daga nan kuma ya shiga firgici da rayuwarsa,” in ji Horacio Acosta.

“Harsashi ɗaya ne ya rage a cikin bindigarsa ta harba-ruga, ga shi ba a iya tafiya, kuma a tsammanin sa babu wanda zai neme shi kwata-kwata,” in ji Horacio Acosta, ƙanin wanda aka ceto.

Jhonattan Acosta ba gatari a hannunsa, babu fitila a lokacin da ya ɓata, haka ya riƙa amfani da takalminsa wurin tarar ruwan sama da zai riƙa sha.

Ya shaida wa ‘yan uwansa yadda ya riƙa arangama da dabbobi masu cin naman mutum ciki har da damisa.

Ya ce akwai wani lokaci da Jhonattan Acosta ya yi amfani da harsashinsa na ƙarshe wajen tsorata wata tawagar kyarkeci – wata dabba mai kama da alade da ake samu a Kudancin Amurka.

Bayan kwana 31, ya jiyo motsin masu bincike kimanin mita 300 nesa da shi, haka ya riƙa ɗingishi ta cikin ƙayoyin daji, ya riƙa ihu domin su jiyo shi.

Horacio ya ce an gano ɗan uwansa ne tare da wasu mutum huɗu. “Wani mutum ne ya taho a guje ya shaida mana cewa an gano ɗan uwana. Wannan wata baiwa ce.”

A cewar ɗan uwan, Jhonattan ya yanke shawarar daina farauta bayan wannan baƙar wuya da ya sha.

“Zai zo ya yi kiɗa domin ya yi godiya ga Allah. Ya yi wa Ubangiji alƙawari cewa in ya cece shi zai yi masa godiya, ina ga zai cika alƙawarin ne,” in ji ɗan uwansa da ya yi kaɗa jita.

A gefe ɗaya kuma ‘yan sanda sun ce za su tambayi sauran mutanen da suke tare kan yadda aka yi ya ɓata. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here